Dalilin da yasa ban halarci faretin bikin yancin kai ba - Saraki

Dalilin da yasa ban halarci faretin bikin yancin kai ba - Saraki

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki yayi bayani kan dalilinsa na kin halartan faretin ranar yancin kai wanda aka gudanar a filin taro na Eagles Square ake babban birnin tarayya Abuja, a ranar Litinin, 1 ga watan Oktoba.

A cewar Saraki ya kasance a wajen Abuja ne inda yake gudanar da wasu muhimman ayyukan siyasa a matsayinsa na dan takarar kujeran shugaban kasa wanda ke burin mallakar tikitin jam’iyyar PDP a zaben fidda gwani da za’a yi a karshen mako.

Ya kuma bayyana cewa an gudanar da zaben fidda gwani na jiharsa a jiya ne wanda dole ana bukatar kasancewarsa a wajen.

Dalilin da yasa ban halarci faretin bikin yancin kai ba - Saraki

Dalilin da yasa ban halarci faretin bikin yancin kai ba - Saraki
Source: Depositphotos

Hadimin Saraki na musamman a kafofin watsa labarai, Yusuph Olaniyonu wanda yayi Magana a madadinsa yace shugaban nasa bai kasance a wajen taron ba saboda zai gana da ýaýan jam’iyya na Kogi domin babban taron PDP na kasa.

A cewarsa wadannan muhimman ayyukan siyasar guda biyu na bukatar hankalin shugaban majalisar dattawan.

KU KARANTA KUMA: Abin da ya sa ba zan koma Majalisar Dattawa ba - Sanata Ben Bruce

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Bukola Saraki, shugaban majalisar dattawa da Yakbu Dogara, kakakin majalisar wakilai basu halarci Eagle Square Abuja ba inda ake bikin shekaru 58 da samun yancin kan Najeriya wanda manyan masu fada aji da jiga-jigan kasar suka halarta.

Wadanda suka halarci faretin sun hada da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da maaimakinsa, Yemi Osinbajo, Walter Onnoghen, alkalin alkalan Najeriya, da tsohon shugaban kasa Yakubu Gowon, da sauran manyan masu fada aji.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel