Tonon Silili: Gwamna Ajimobi bai yi NYSC ba yake neman zama Sanata - Shittu

Tonon Silili: Gwamna Ajimobi bai yi NYSC ba yake neman zama Sanata - Shittu

Mun samu labari jiya cewa Ministan sadarwa na kasar nan Mista Adebayor Shittu ya fallasa Gwamnan Jihar Oyo watau Abiola Ajimobi inda yace Gwamnan bai taba yin aikin bautar kasa na NYSC ba.

Tonon Silili: Gwamna Ajimobi bai yi NYSC ba yake neman zama Sanata - Shittu

Shittu yace Ajimobi bai yi aikin hidimar kasa ba kuma yak neman takara
Source: Depositphotos

Idan ba ku manta ba an dakatar da Ministan daga neman takarar Gwamna a karkashin Jam’iyyar APC ne saboda bai yi wa kasa hidima ba a lokacin da ya kammala Jami’a. Hakan ta sa babban Ministan ya fito yana mai kare kan sa.

KU KARANTA: Tsohon ministan Abuja ya zama dan takarar gwamna a PDP

Adebayor Shittu yace kamar yadda bai yi NYSC ba, haka Gwamna Abiola Ajimobi yake neman kujerar Sanata ba tare da yayi bautar kasa ba. Ministan yayi wannan tononsilili ne a gaban gidan Talabijin na Channelsa TV Ranar Lahadi.

Ministan yana cikin wadanda Jam’iyyar APC ta haramtawa takara a 2019 don haka ya fito yace in dai don bai da takardun NYSC ne to Gwamnan Jihar wanda yake kan mulki yanzu ma bai da takardun da za su nuna cewa yayi NYSC a baya.

Shittu yana harin kujerar Gwamnan Jihar Oyo ne a zaben 2019 inda yace Gwamnan ne ke kokarin taka masa burki domin gudun ya daure sa idan ya hau Gwamna. Ministar harkokin mata tana cikin wadanda aka hana takara har ta bar APC.

Kun kuma ji cewa Sanata Ben Murray Bruce na PDP yayi ban kwana da aikin Majalisar Tarayyar inda ya nuna godiya ga mutanen Mazabar sa. Sanatan yace zai ba wasu dama kujerar ta zo kan su a zaben 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel