Abin da ya sa ba zan koma Majalisar Dattawa ba - Sanata Ben Bruce

Abin da ya sa ba zan koma Majalisar Dattawa ba - Sanata Ben Bruce

Labari ya iso mana cewa Babban Sanatan nan na Jam'iyyar PDP Ben Murray Bruce ya tabbatar da cewa ba zai nemi takara a zaben 2019 ba. Sanatan yace yayi bakin kokarin sa a Majalisa kuma yayi ya gama.

Abin da ya sa ba zan koma Majalisar Dattawa ba - Sanata Ben Bruce

Sanata Ben Bruce yayi ban kwana da Majalisar Dattawa

Sanatan na Bayelsa ta gabas wanda an saba jin muryar sa a Majalisar Dattawa ya rubutawa Jam'iyyar sa ta PDP wasika inda yace ba zai nemi tazarce a kan kujerar ba. Bruce yace zai ba wasu 'Yan siyasar wasu Yankin dama su dana kujerar a 2019 kamar yadda aka saba yi.

Bruce yace ya tuntubi mutanen sa don haka ya lura cewa abin da ya fi shi ne ya ci girma domin mutanen wasu Yankin su wakilci Bayelsa ta Gabas a Majalisar kamar yadda aka dade ana yi a Jihar. Yanzu dai za a fito da Sanata ne daga wata karamar Hukumar.

KU KARANTA: Sanata ‘Dan shekaru 75 zai yi takarar Gwamnan Jihar Filato a 2019

'Dan Majalisar ya godewa mutanen sa da su ka ba sa dama ya wakilce su na shekaru 4 a matsayin Sanatan Najeriya. Sanata Bruce ya wakilci Yankin Brass da Bayelsa ta Gabas ne tun daga 2015 inda yace yayi iyaka bakin kokarin sa a Majalisar wajen kare jama’an sa.

Sanata Bruce yayi ban kwana da aikin Majalisar Tarayyar inda ya nuna godiya ga tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan da Shugaban PDP na kasa Uche Secondus da kuma Gwannan Jihar Bayelsa Seriake Dickson. Sanatan yace saboda mutane dama yake wannan aiki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel