Atiku Abubakar: Na tsamo iyalai 45,000 daga kangin talauci a Nigeria

Atiku Abubakar: Na tsamo iyalai 45,000 daga kangin talauci a Nigeria

- Alhaji Atiku Abubakar, ya ce ya tsamo iyalai 45,000 daga kangin talaucin da suke ciki a Nigeria

- Ya samu wannan nasarar ne ta baiwa mata rance daga kamfanin 'yan kasuwa da ya kafa

- Ya kuma ce akwai shirin da ya kuduri yi na daukar ma'aikata miliyan 12 idan har ya zama shugaban kasa

Tshohon shugaban kasar Nigeria, kuma wanda ke son tsayawa takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce ya tsamo iyalai 45,000 daga kangin talaucin da suke ciki a Nigeria.

Atiku ya bayyana hakan a wani taron musayar ra'ayi da manema labarai da aka shirya kan tsayawa takarar shugaban kasa, wanda kungiyar hadin kan kungiyoyin Nigeria UNG ta shirya a babban birnin tarayya Abuja.

Ya ce ya samu nasarar cimma hakan ne ta hanyar wani bankin 'yan kasuwa da ya samar, yana mai cewa ya kuma umurcim bankin da ya baiwa mata kashi 80 na basussuakn da ya ke bayarwa "da zummar cewa ta hanyar bunkasa rayuwarsu ne kawai zai iya tsamo iyalai daga talauci".

Atiku Abubakar: Na tsamo iyalai 45,000 daga kangin talauci a Nigeria

Atiku Abubakar: Na tsamo iyalai 45,000 daga kangin talauci a Nigeria

KARANTA WANNAN: Manyan matsafa 13 a Arewa sun shiga hannun jami'an tsaron Najeriya

"Na mallaki bankunan 'yan kasuwa da dama a kasar nan, wadanda suka samu nasarar aiwatar da duk wani aiki da na sanya su. Ina aiki da jama'a daga Bangladesh saboda sunfi kowa kwarewa idan har aka zo bangaren kula da harkokin bankunan 'yan kasuwa.

"Sannan babbar hanyar tsamo iyalai daga talauci ba zai wuce bunkasa rayuwar mata ba. Saboda hakane ma na umurci bankin da ya baiwa mata kaso 80 na dukkanin basussukan da zai dinka bayarwa, don ba su damar dogaro da kawunansu."

Atiku ya jaddada muhimmancin jawo masu saka hannu jari daga kasashen ketare zuwa Nigeria don tallafawa wadanda suka kammala karatu ta hanyoyin da za su dogara da kawunansu, yana mai cewa akwai shirin da ya kuduri yi na daukar ma'aikata miliyan 12 idan har ya zama shugaban kasa.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel