Magoya bayan Ambode sunyi zanga-zanga a kofar gidan Tinubu

Magoya bayan Ambode sunyi zanga-zanga a kofar gidan Tinubu

Magoya bayan gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode sunyi tattaki zuwa kofar gidan Tinubu a ranar Litinin dauke da alluna masu dauke da sakonni daban-daban. Sai dai basu samu damr shiga gidan ba saboda akwai jami'an tsaro masu yawa da ke gadi.

Wasu daga cikin magoya bayan gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode sun dunguma zuwa gidan shigaban jam'iyyar All Progressives Party (APC) na kasa da ke Bourdillon Street a unguwar Ikoyi da ke Legas.

Magoya bayan Ambode sunyi zanga-zanga a kofar gidan Tinubu

Magoya bayan Ambode sunyi zanga-zanga a kofar gidan Tinubu
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Mata ta da Buhari ne kadai masu gidana a duniya - Gwamnan PDP

Masu zanga-zangar na dauke da alluna masu dauke da hotunan Ambode da wasu sakonni inda su kayi cincirindo a kofar shiga gidan Bola Tinubu a ranar Litinin sai dai basu samu ikon shiga harabar gidan ba domin akwai jami'an tsaro dauke da bindigogi da ke gadi.

Hakan yasa masu zanga-zangar suka koma tsallaken titi suna fuskantar kofar gidan suna kade-kade da raye-raye kana suna nuna hotunnan Ambode wanda hakan ke nufin shi su ke son Tinubu ya marawa baya.

Cikin kwanakin nan Ambode yana fuskantar barazanar rasa tikitin takarar jam'iyyar APC domin Tinubu da galibin 'yan majalisar jihar Legas sun bayyana goyon bayansu ga Babajide Sanwo-Olu a matsayin wanda zai yiwa jam'iyyar takara a 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel