2019: Fintiri ya lashe zaben fidda gwani a jihar Adamawa

2019: Fintiri ya lashe zaben fidda gwani a jihar Adamawa

Tsohon Kakakin Majalisar Jihar Adamawa kuma gwamna mai rikon kwarya, Alhaji Ahmadu Finitiri ya lashe zaben fidda gwani na gwamna da jam'iyyar PDP ta gudanar a jihar.

Finitiri ya fafata da wasu 'yan takara hudu ne inda ya samu kuri'u 1,656 ya kuma kayar da su.

A yayin da ya ke sanar da sakamakon zaben, jami'in zaben, Alhaji Adamu Shuaibu ya ce Fintiri ya samu kuri'u 1,656 yayin da mai biye masa Ambasada Mohammed Jameel ya samu kuri'u 465.

2019: Fintiri ya lashe zaben fidda gwani a jihar Adamawa

2019: Fintiri ya lashe zaben fidda gwani a jihar Adamawa
Source: Twitter

Mr Bala Ngilari ya samu kuri'u 78, sai Mr Aliyu Umar ya samu kuri'u takwas yayin da Dr Umar Ardo ya samu kuri'a daya tilo.

DUBA WANNAN: Jam'iyyar PDP: Saraki ya maka Atiku da Tambuwal da kasa a zaben jin ra'ayi

Sauran 'yan takarar guda biyu, Alhaji Sa’ad Tahir and Alhaji Adamu Modibbo sun janye tun kafin a fara zaben fidda gwanin.

A jawabin da ya yi bayan an sanar da sakamakon zaben, Fintiri ya mika godiyarsa ga masu ruwa da tsaki a jam'iyyar musamman tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da Bamanga Tukur da Farfesa Jibrin Aminu da sauransu.

Fintiri ya kuma mika godiyarsa da deleget din jam'iyyar tare da daukar alkawarin kawo cigaba mai ma'ana a jihar.

Daga karshe ya yi kira ga magoya bayansa da 'yan jam'iyyar su taimaka masa domin ya yi nasarar komawa gidan gwamnati da ke Yola a zaben 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel