Dan takarar gwamna ya bawa Buhari shawarar abinda ya dace a yiwa marigayi Baba-Ari

Dan takarar gwamna ya bawa Buhari shawarar abinda ya dace a yiwa marigayi Baba-Ari

- Dan takarar gwamna a Labour Party na jihar Kwara, Issa Aremu ya shawarci shugaba Buhari ya karama matukin jirgin da ya rasu a Abuja da lambar yabo na kasa

- Aremu ya jinjinawa dakarun Sojin Saman Najeriya saboda irin sadaukarwarsu wadda ya ce abin koyi ne ga sauran 'yan kasa

Dan takarar gwamna karkashin jam'iyyar Labour Party a zaben 2019 a jihar Kwara, Issa Aremu ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya karramar marigayi Bello Baba-Ari da lambar yabo na kasa.

Mr Baba-Ari ya rasu ne a hatsarin jiragen saman Sojin Najeriya da ya afku a Katampe da ke Abuja yayin da matukan jiragen ke shirye-shiryen bukukuwan zagayowar ranar samun 'yancin Najeriya.

Wani dan takarar gwamna ya shawarci Buhari ya karrama matukin jirgin da ya rasu a Abuja

Wani dan takarar gwamna ya shawarci Buhari ya karrama matukin jirgin da ya rasu a Abuja
Source: Twitter

DUBA WANNAN: PDP ta bani cin hancin makudan miliyoyi don na bar APC - Sanatar Arewa

Mr Aremu ya yi wannnan kirar ne a ranar Litinin 1 ga watan Oktoba yayin bukukuwar zagayowar ranar 'yancin da jam'iyyarsa ta shirya a Ilorin kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Ya ce marigayi Baba-Ari ya sadaukar da rayuwarsa ne yayin yiwa kasarsa hidima tare da sauran matukan jirgin da suka yi rauni, inda ya kara da cewa irin wannan sadaukarwar abin koyi ne ga sauran 'yan Najeriya.

"Akwai bukatar ayi murnar zagoyar samun 'yancin Najeriya cikin kyakyawar yanayin kamar yadda dakarun sojin saman Najeriya su kayi," inji Aremu.

Dan takarar gwamnan kuma ya cacaki wasu gwamnoni da suka bayar da umurnin tsagaita bukukuwar zagayowar 'yancin Najeriya amma sukan kashe kudade sosai idan ranar zagoyowar haihuwarsu ko na yaransu ya taso sai su kashe kudaden jiha.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel