2019: Gwamna Abubakar ya fara tunanin barin APC kafin zabe

2019: Gwamna Abubakar ya fara tunanin barin APC kafin zabe

Yanzu mun samu labari cewa ana kishin-kishin din Gwamnan Jihar Bauchi Mohammed Abubakar Esq. na neman tserewa daga Jam’iyyar APC mai mulki a lokacin da ake shirin zaben fitar da gwani.

2019: Gwamna Abubakar ya fara tunanin barin APC kafin zabe

Akwai yiwuwar Gwamnan Bauchi ya bar APC idan ya sha kunya
Source: Depositphotos

Jaridar 247Reporters ta rahoto cewa Gwamna Mohammed Abubakar na neman sauya-sheka zuwa Jam’iyyar adawa ta SDP ko PDP. Sai dai yanzu har Jam’iyyar PDP ta tsaida ‘Dan takarar Gwamnan ta a zaben da za ayi a shekarar 2019.

Hakan na zuwa ne bayan abubuwa sun fara sukurkucewa Gwamnan a Jam’iyyar APC. Yanzu haka dai akwai manyan ‘Yan siyasan da ke kokarin karbe ragamar mulkin Jihar daga hannun Gwamna Mohammed Abubakar a APC.

KU KARANTA: 2019: Jam’iyyar APC za ta zabi ‘Yan takarar da za a ba tutan a zaben Gwamnoni

Jam’iyyar ta APC mai mulki ta rabu kashi biyu yanzu inda wasu ke kukan cewa Gwamnan ba yayi da su tun da ya hau mulki. Daga cikin masu harin kujerar Gwamnan akwai tsohon Ministan lafiyan kasar Dr. Muhammad Ali Pate.

Kawo yanzu dai Jam'iyyar APC ta tsaida tsohon Minista Bala Mohammed ne a matsayin wanda zai yi takara da APC a zaben shekara mai zuwa. Bala Mohammed tsohon Sanata ne kuma yayi Minista na babban Birnin Tarayya Abuja.

A baya masu neman kujerar Gwamna a Bauchi sun rubuta wasika zuwa Hedikwatar Jam’iyyar APC inda su kayi kira ga Shugaban Jam’iyya da kuma Shugaban kasa ta kutso kai cikin rikicin Jihar wanda hakan ya sa aka sake tsarin zaben.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel