Ogboru ya lashe zaben fidda gwani na gwamna a jihar Delta

Ogboru ya lashe zaben fidda gwani na gwamna a jihar Delta

- Jam'iyyar APC ta fada cikin ruduna a jihar Delta

- Bangarorin jam'iyyar biyu duk sun gudanar da zaben cikin gida sun fitar da 'yan takara

- Dukkan 'yan takarar biyu na ikirarin nasarar lashe zaben

Mun samu daga Punch cewar Great Ogboru ya lashe zaben fidda gwani na kujerar gwamna a jam'iyyar APC a jihar Delta da aka gudanar a Kwallejin Ilimi da ke Asaba babban birnin jihar Delta.

Wannan sanarwan yana zuwa ne sa'o'i kadan bayan an ruwaito cewa Farfesa Pat Utomi shima ya lashe zaben fidda gwanin da wata bangare na jam'iyyar ta APC karkashin jagorancin Cif Cyril Ogodo ta gudanar.

Ogboru ya lashe zaben fidda gwani na gwamna a jihar Delta

Ogboru ya lashe zaben fidda gwani na gwamna a jihar Delta
Source: Twitter

Ogboru ya yi nasarar ne a zaben fidda gwani da bangaren Jones Erue ta shirya karkashin jagorancin kwamitin zabe na Janar Lawrence Onoja. Ya yi nasarar lashe zaben ne bayan ya yi takarar sau hudu a baya.

DUBA WANNAN: Jam'iyyar PDP: Saraki ya maka Atiku da Tambuwal da kasa a zaben jin ra'ayi

A yayin da Onoja ke sanar da sakamakon zaben da aka fara tun ranar Lahadi, ya ce Ogboru ya yi nasarar lashe zaben ne inda ya samu kuri'u 3,292 yayin da mai biye masa Victor Ochei, ya samu kuri'u 160.

A bangarensa, Pat Utomi ya samu kuri'u 26 yayin da mai biye masa Dr. Cairo Ojougboh ya samu kuri'u 12.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel