An kashe mutane biyu a yayin da rikici ya barke a yayin zaben fitar dan takarar gwamnan APC

An kashe mutane biyu a yayin da rikici ya barke a yayin zaben fitar dan takarar gwamnan APC

Akalla mutane biyu ne suka rigamu gidan gaskiya a sakamakon rikici daya barke a yayin da ake gudanar da zaben fitar da dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jahar Akwa Ibom, kamar yadda jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito daga cikin mutanen da aka kashe akwai wani mai suna Ukeme Efanga, wanda aka kashe shi a karamar hukumar Uruan ta jahar, a yayin da yan bindiga suka yi kokarin kwatar akwatunan zabe.

KU KARANTA: Takarar gwamna: Nuhu Ribadu ya yi amai ya lashe game da zaben fidda gwani

An kashe Efanga ne a daidai lokacin da yayi kokarin hana yana bindigan kwace akwatunan zabe da sauran kayayyakin zaben, sai kuma wani mai suna Emmanuel Asuquo wanda shima aka kashe shi a karamar hukumar Uyo.

Wasu yan bindiga da suka diran ma sakatariyar jam’iyyar APC ta jahar ne dake kan titin Ikot Ekpene suka bindige Asuquo a lokacin da magoya bayan jam’iyyar APC suka ja daga da yan wasu yan daban siyasa da suka yi kokarin karkatar da kayan zaben da za’a kai kananan hukumomin Akwa Ibom ta kudu da Arewa.

Wani shaidan gani da ido yace: “Matsalar ta faro ne a daidai lokacin da magoya bayan jam’iyyar APC da wasu wakilan yan takarar gwamnan jahar suke cacar baki dangane da karbar kayan zabe, sai aka shigar da wasu wakilan yan takarar cikin ayarin motocin wani dan takarar gwamnan jahar.

“Yayin da wasu wakilan kuma aka fatattakesu, daga nan ne da sauran jama’a dake wajen suka ce babu wanda ya isa ya tafi da kayan zaben ba tare da daukan sauran wakilan yan takarkarun ba, suna cewa ana shirin karkatar da kayan zaben ne.

“Daga nan kuma sai jama’a suka tare hanyar da ayarin motocin zasu wuce, suna kira ga yansandan dake rakiyar motocin da kodai su shigar da sauran wakilan yan takarar cikin motocin ko kuma kowa ya sauka daga motocin, kwatsam sai muka ji karan harbe harbe.” Inji shi.

Duk kokarin da majiyarmu ta yin a jin ta bakin kaakakin rundunar Yansandan jahar, Odiko Macdon ya gagara sakamakon baya daukan wayan majiyar tamu, kuma bai amsa wasikar ko ta kwana da ya aika masa ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel