Jami’an tsaro sun garkame dakin taron da PDP zata fitar da dan takarar gwamna a Kano

Jami’an tsaro sun garkame dakin taron da PDP zata fitar da dan takarar gwamna a Kano

An samu cikas game da zaben fitar da dan takarar gwamnan jahar Kano a inuwar jam’iyyar PDP, inda wasu jami’an Yansanda mota mota suka durfafi wajen da ake gudanar da wannan zabe suka kuma garkame ta, bas hi ba fita.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Litinin 1 ga watan Oktoba a dandalin Marahaba silma inda jam’iyyar ke gudanar da zaben fitar da gwanin da zai tsaya mata takarar gwamnan jahar.

KU KARANTA: Najeriya ta cika shekaru 58 da samun yancin kai: Jerin shuwagabanninta tun daga 1960

Jami’an tsaro sun garkame dakin taron da PDP zata fitar da dan takarar gwamna a Kano

Yansanda
Source: Facebook

Sai dai rundunar Yansandan jahar ta bakin kaakakinta, Magaji Musa Majia ya bayyana dalilin da yasa suka garkame Marhaba silma tare da hana wakilan da zasu kada kuri’a a zaben fitar da dan takarar shiga wajen taron.

Majia yace rundunar Yansandan jahar Kano tana biyayya ne ga umarnin Kotu data haramta shugabancin jam’iyyar PDP a karkashin sabon shugabanta na riko, Rabiu Suleiman Bichi, bayan wasu yayan jam’iyyar sun shigar da kara a gaban Kotun suna kalubalantar shugabancin nasa.

“Kotu ta bada umarnin dakatar da duk wani taron siyasa a jam’iyyar PDP sakamakon rikicin tsakar gida daya dabaibayeta.” Inji kaakakin rundunar Yansandan jahar Kano, Magaji Majia.

Sakamakon wannan matsala da aka samu, sai wakilan jam’iyyar da zasu kada kuri’u a wannan zabe suka garzaya zuwa babban ofishin Kwankwasiyya dake cikin garin Kano don yin wata ganawar gaggawa tare da lalubo matakin da zasu dauka na gaba.

Bayan kammala wannan ganawa ne sai suka yanke shawarar cigaba da gudanar da zaben fitar da dan takarar, amma fa wannan karon a sabon ofishin kwankwasiyya dake unguwar Lugard Avenue.

Jami’an tsaro sun garkame dakin taron da PDP zata fitar da dan takarar gwamna a Kano

Yansanda
Source: Facebook

Jami’an tsaro sun garkame dakin taron da PDP zata fitar da dan takarar gwamna a Kano

Yan Kwankwasiyya
Source: Facebook

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa.

Mungode da kasancewanku tare da mu

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel