Wani na hannun Jonathan na neman jefa shi cikin wata sabuwar cakwakiya

Wani na hannun Jonathan na neman jefa shi cikin wata sabuwar cakwakiya

- Wani na hannun Jonathan na neman jefa shi cikin wata sabuwar cakwakiya

- Yace dukkan kudin da ake tuhumar sa da sacewa, Jonathan ne ya sa shi

- Yanzu haka yana fuskantar shari'a ne a gaban kotu

Mataimaki na musamman akan harkokin cikin gida ga tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan lokacin mulkin sa mai suna Dakta Waripamo-Owei Dudafa, a jiya ya kara jadda cewa shi fa dukkan kudaden da ake bincikar sa da ci, sa shi akayi.

Wani na hannun Jonathan na neman jefa shi cikin wata sabuwar cakwakiya

Wani na hannun Jonathan na neman jefa shi cikin wata sabuwar cakwakiya
Source: Depositphotos

Dakta Waripamo-Owei Dudafa ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar Dakta Goodluck Jonathan da matar sa Patience Goodluck sune suka sa shi ya cire kudaden kuma yana ganin ya kamata ayi masa adalci.

Legit.ng ta samu cewa ana tuhumar Dakta Waripamo-Owei Dudafa da wani na hannun damar sa mai suna Iwejuo Nna Joseph a wata babbar kotun tarayya a garin Legas bisa yin sama da fadi da Naira biliyan 1 da dubu dari shidda.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa an gurfanar da wadanda ake tuhumar a kotun a baya tun cikin watan Yunin shekarar 2016 akan zargin da ake yi masu, inda su kuma suka musanta zarge-zargen.

A wani labarin kuma, Jami'an 'yan sandan Najeriya dake kula da shiyyar jihar Ribas sun sanar da samun nasarar cafke wani babban malamin addinin kirista da kuma wasu mata masu ciki da suka kai akalla 16 bisa zargin cinikayyar jarirai.

Wannan dai kamar yadda muka samu daga bakin kwamishinan 'yan sandan jihar Zaki Ahmed, ya biyo bayan wani samame ne da jami'an 'yan sandan suka kai a wani gidan dake zargin ana yiwa mata ciki sannan kuma su saida jariran a garin Fatakwal.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mungode da kasancewarku tare da mu

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel