Duk karya ce: 'Ambode ya tabbatar da cewa APC jam'iyyar mayaudara ce'

Duk karya ce: 'Ambode ya tabbatar da cewa APC jam'iyyar mayaudara ce'

- Gwamnan Legas, Ambode ya tonawa jam'iyyar APC asiri

- PDP tace maganar da Ambode ya fada dame da APC gaskiya ne

- PDP ta ce ya kamata al'ummar Najeriya ta guji APC

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Lahadi da ta gabata ta ce yanzu dai kam gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode ya tabbatar wa da duniya cewa jam'iyyar All Progressives Congress (APC), taron mayaudara ne kawai.

Duk karya ce: 'Ambode ya tabbatar da cewa APC jam'iyyar mayaudara ce'

Duk karya ce: 'Ambode ya tabbatar da cewa APC jam'iyyar mayaudara ce'
Source: Twitter

KU KARANTA: An sace motoci 5 cike da mutane a Birnin Gwari

A jiya ne dai gwamnan na Legas ya kira wani taron manema labarai na kasa-da-kasa inda ya bayyana abokin hamayyar sa a zaben fitar da gwani da jam'iyyar zata gudanar a jihar Babajide Sanwo-Olu a matsayin tsohon dan damfara kuma mai tabin hankali.

Legit.ng dai ta samu cewa gwamnan na jihar Legas yanzu haka yana fuskantar matsala bayan da ya shiga tsaka mai wuya biyo bayan sabanin da ya samu da jagoran jam'iyyar APC a jihar Cif Bola Tinubu.

Mai magana da yawun jam'iyyar ta PDP Mista Kola Ologbondiyan ya kara da cewa duba da irin hakan ne yake kara kira da 'yan jam'iyyar da ma sauran 'yan Najeriya da su guji jam'iyyar a zabukan 2019 masu zuwa.

A wani labarin kuma, Jam'iyya mai mulki a Najeriya ta All Progressives Congress (APC) ta ce abun kunya ne a ce jam'iyyar tana a cikin aljihun mutum daya kuma wannan mutumin ya kasance shine Gwamnan jihar Ribas Mista Nyeson Wike.

Jam'iyyar ta cigaba da cewa kawo yanzu dai dukkan duniya ta tabbatar da cewa gwamnan na Ribas shine shugaban jam'iyyar ta PDP sannan kuma shine mai magana da yawun ta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel