Kuma dai: An gano wani gwamnan APC da bai yi bautar kasa ba

Kuma dai: An gano wani gwamnan APC da bai yi bautar kasa ba

- An gano wani gwamnan APC da bai yi bautar kasa ba

- Ana zargin Gwamnan Ogun Ajimobi Abiola bai yi NYSC ba

- Ministan sadarwa ne yayi wannan zargin

Babban ministan harkokin sadarwa a gwamnatin shugaba Buhari ta tarayyar Najeriya, Mista Adebayo Shittu ya yi ikirarin cewa gwamnan jihar Oyo mai barin gado Mista Abiola Ajimobi bai yi shirin nan na bautawa kasa ba na National Youth Service Corps (NYSC) a turance.

Kuma dai: An gano wani gwamnan APC da bai yi bautar kasa ba

Kuma dai: An gano wani gwamnan APC da bai yi bautar kasa ba
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Wani dattijon Arewa yayi wa Buhari kaca-kaca

Ministan dai yayi wannan zargin ne a lokacin da ake fira da shi a gidan talabijin mai zaman kan sa na Channels TV inda ya kuma kara da cewa gwamnan baya son sa ko kadan daman can.

Legit.ng ta samu cewa Mista Shittu ya ce" Gwamna Ajimobi baya kauna ta ko kadan shi ne dalilin da ya sa ma ya yi kulle-kulle har sai da ya sa aka wancalar da dani daga jerin 'yan takarar kujerar gwamnan jihar domin a tunanin sa idan na zama gwamna zan sa a daure shi".

Ya kuma kara da cewa idan har ana maganar yin bautar kasa ne kuma, to tabbas shima gwaman muna da yakinin bai yi ba amma lokaci muke jira da za mu fallasa lamarin kowa ya ji.

A wani labarin kuma, Jam'iyya mai mulki a Najeriya ta All Progressives Congress (APC) ta ce abun kunya ne a ce jam'iyyar tana a cikin aljihun mutum daya kuma wannan mutumin ya kasance shine Gwamnan jihar Ribas Mista Nyeson Wike.

Jam'iyyar ta cigaba da cewa kawo yanzu dai dukkan duniya ta tabbatar da cewa gwamnan na Ribas shine shugaban jam'iyyar ta PDP sannan kuma shine mai magana da yawun ta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel