Yanzu Yanzu: Saraki da Dogara basu halarci faretin ranar yancin kai ba

Yanzu Yanzu: Saraki da Dogara basu halarci faretin ranar yancin kai ba

- Shugaban majalisar dattawa BukolaSaraki bai halarci faretin ranar yancin kai ba

- Haka ma takwaransa na majalisar wakilai, Dogara bai hallara a

- Shugaban kasa Buhari da manyan masu fada a ji suna Eagle Square Abuja inda taron ke gudana

- Babu wani dalili da aka bayar kan rashin zuwan nasu a lokacin wannan rahoton

Bukola Saraki, shuaban majalisar dattawa da Yakbu Dogara, kakakin majalisar wakilai basu halarci Eagle Square Abuja ba inda ake bikin shekaru 58 da samun yancin kan Najeriya wanda manyan masu fada aji da jiga-jigan kasar suka halarta.

Wadanda suka halarci faretin sun hada da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da maaimakinsa, Yemi Osinbajo, Walter Onnoghen, alkalin alkalan Najeriya, da tsohon shugaban kasa Yakubu Gowon, da sauran manyan masu fada aji.

Yanzu Yanzu: Saraki da Dogara basu halarci faretin ranar yancin kai ba

Yanzu Yanzu: Saraki da Dogara basu halarci faretin ranar yancin kai ba
Source: Depositphotos

Sojin kasar za su yifareti don girmamawa sannan a fito da hotuna dake nuni ga tarihin Najeriya da kuma liyaar ranar yancin kai.

KU KARANTA KUMA: Shekaru 58 da samun yanci: Buhari yayi gagarumin jawabi akan INEC, zabe na gaskiya da amana

Duk kokari da akayi domin Magana gaYusuph Olaniyonu, kakakin Saraki bai samu ba, kakakin Dogara kuma, Turaki Hassan yace baida masaniyar ko an gayyaci ubanidansa ko kuma dalilin day a hana shi zuwa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel