Dakarun sojojin Najeriya sun gano inda 'yan Boko Haram ke gudanar da tarukan su

Dakarun sojojin Najeriya sun gano inda 'yan Boko Haram ke gudanar da tarukan su

- Dakarun sojojin Najeriya sun gano babban dakin taron 'yan Boko Haram

- Dakin taron yana a kauyen Jabullam a can jihar ta Borno

- Tuni dai har sojojin sunyi raga-raga da shi

Dakarun sojojin saman Najeriya dake a rundunar nan dake yaki da 'yan ta'addan Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin Najeriya sun sanar da samun nasarar gano wani babban dakin taron 'yan ta'addan a kauyen Jabullam a can jihar ta Borno tare kuma da yin raga-raga da shi.

Dakarun sojojin Najeriya sun gano inda 'yan Boko Haram ke gudanar da tarukan su

Dakarun sojojin Najeriya sun gano inda 'yan Boko Haram ke gudanar da tarukan su
Source: Facebook

KU KARANTA: Masana kimiyya sun yi hasashen lokacin da za'ayi tashin kiyama

Kwamandojin rundunar dake kula da harkokin yada labaran su ne dai, Air Commodore Ibikunle Daramola ya sanarwa da manema labarai hakan a garin Abuja lokacin da yake zantawa da su.

Legit.ng ta samu haka zalika cewa Air Commodore Ibikunle Daramola yace biyo bayan gano wurin taron ne sai jami'an su suka dauki harama inda kafin ka kifta ido duk sun lalata wurin tare da ma gine-ginen da ke makwaftaka da shi.

A wani labarin kuma, Jami'an 'yan sandan Najeriya dake kula da shiyyar jihar Ribas sun sanar da samun nasarar cafke wani babban malamin addinin kirista da kuma wasu mata masu ciki da suka kai akalla 16 bisa zargin cinikayyar jarirai.

Wannan dai kamar yadda muka samu daga bakin kwamishinan 'yan sandan jihar Zaki Ahmed, ya biyo bayan wani samame ne da jami'an 'yan sandan suka kai a wani gidan dake zargin ana yiwa mata ciki sannan kuma su saida jariran a garin Fatakwal.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel