Abun kunya ne ace wai PDP tana cikin aljihun Gwamna Wike - APC

Abun kunya ne ace wai PDP tana cikin aljihun Gwamna Wike - APC

- PDP jam'iyyar mutum daya ce - APC

- APC tace PDP ta Gwamna Wike ce

- Tace wannan babban abub kunya ne

Jam'iyya mai mulki a Najeriya ta All Progressives Congress (APC) ta ce abun kunya ne a ce jam'iyyar tana a cikin aljihun mutum daya kuma wannan mutumin ya kasance shine Gwamnan jihar Ribas Mista Nyeson Wike.

Abun kunya ne ace wai PDP tana cikin aljihun Gwamna Wike - APC

Abun kunya ne ace wai PDP tana cikin aljihun Gwamna Wike - APC
Source: Facebook

KU KARANTA: Yan Boko Haram sun fara kashe kan su da kan su

Jam'iyyar ta cigaba da cewa kawo yanzu dai dukkan duniya ta tabbatar da cewa gwamnan na Ribas shine shugaban jam'iyyar ta PDP sannan kuma shine mai magana da yawun ta.

Legit.ng ta samu cewa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) dai tayi wannan ikirarin ne a ta bakin mai magana da yawun ta na rikon kwarya, Yekini Nabena a cikin wata sanarwar manema labarai dauke da sa hannun sa.

A wani labarin kuma, Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Lahadi da ta gabata ta ce yanzu dai kam gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode ya tabbatar wa da duniya cewa jam'iyyar All Progressives Congress (APC), taron mayaudara ne kawai.

A jiya ne dai gwamnan na Legas ya kira wani taron manema labarai na kasa-da-kasa inda ya bayyana abokin hamayyar sa a zaben fitar da gwani da jam'iyyar zata gudanar a jihar Babajide Sanwo-Olu a matsayin tsohon dan damfara kuma mai tabin hankali.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel