Ajimobi ya zata idan na zama Gwamna zai tafi gidan yari - Shittu

Ajimobi ya zata idan na zama Gwamna zai tafi gidan yari - Shittu

Ministan sadarwa, Adebayo Shittu yayi zargin cewa Gwamna Abiola Ajimobi na adawa da kudirinsa na takarar gwamna ne saboda tsoron kada a tura shi gidan yari.

Shittu ya bayyana hakan ne a lokacin wata hira da shirin Sunday Politics na gidan talbijin din Channels TV.

Yace: “Abiola Ajimobi ya zata kuma yana ta fadama magoya bayansa cewa idan Adebayo Shittu yayi nasara zai tafi gidan yari."

Wannan sharhin na zuwa ne yan kwanaki kadan bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta ki tantance ministan a matsayin dan takara a zaben fidda gwani na jihar Oyo.

Ajimobi ya zata idan na zama Gwamna zai tafi gidan yari - Shittu

Ajimobi ya zata idan na zama Gwamna zai tafi gidan yari - Shittu
Source: Depositphotos

Kin tantance shin ya biyo bayan rahoton cewa bai yi wa kasa hidima ba bayan kammala karatun jami’a duk da cewa a lokacin yana da shekaru 25 ne kacal a duniya.

Sai dai ministan yak are kan shi akan haka, nda yace zabar shi da aka yi a matsayin dan majalisa bayan kammala karatunsa daidai yake da yiwa kasa hidima.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan jahar Kaduna ya sha ruwan kuri’u a zaben fitar da gwani na APC

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yi nasarar mallakar tikitin jam’iyyar All Progressive Congress (APC) a matsayin dan takarar kujeran gwamna da kuri’u 2,740,847.

Mista Pius Odudu jami’in jam’iyyar ne ya kaddamar da Ganduje wanda shi kadai ke neman kujerar, a matsayin dan takararya bayan kammala zaben fidda gwani.

Ku tuna cewa jam’iyyar APC a Kano ta yi amfani da zaben fidda gwani na wakilai ne a jihar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel