Zaben fiddan gwani na APC: Ganduje ya samu tikiti da kuri’u miliyan 2.7

Zaben fiddan gwani na APC: Ganduje ya samu tikiti da kuri’u miliyan 2.7

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yi nasarar mallakar tikitin jam’iyyar All Progressive Congress (APC) a matsayin dan takarar kujeran gwamna da kuri’u 2,740,847.

Mista Pius Odudu shugaban zaben ne ya kaddamar da Ganduje wanda shi kadai ke neman kujerar, a matsayin dan takararya bayan kammala zaben fidda gwani.

Ku tuna cewa jam’iyyar APC a Kano ta yi amfani da zaben fidda gwani na wakilai ne a jihar.

Zaben fiddan gwani na APC: Ganuje ya samu tikiti da kuri’u miliyan 2.7

Zaben fiddan gwani na APC: Ganuje ya samu tikiti da kuri’u miliyan 2.7
Source: Depositphotos

Da yake nuna amincewarsa da sakamakon zaben, gwamna Ganduje ya yabi yadda aka gudanar da zaben cikin lumana sannan ya godema mambobin jam’iyyar da sukia marawa tazarcensa baya.

Ganduje wanda yayi Magana ta hannun mataimakinsa, Dr Nasiru Yusuf Gawuna ya karfafa ma mambobin jam’iyyar a fadin kasar gwiwar zabar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019 mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Surikin IBB Sunny Okogwu ya mutu a asibitin Abuja

A wani lamari makamancin haka, mun ji cewa jimillan yayan jam’iyyar APC kuma wakilan da suka kada ma gwamnan jahar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai kuri’u a zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC na takarar gwamnan jahar, kamar yadda kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Lahadi, 30 ga watan satumba ne aka gudanar da wannan zabe a dandanlin Murtala dake garin Kaduna, inda wakilai dubu uku da dari bakwai da tamanin da biyu (3, 782) daga kananan hukumomi ashirin da uku suka kada kuri’a.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel