Ranar yanci: Buhari yayi alkawarin aiki don zaman lafiya da cigaban Najeriya

Ranar yanci: Buhari yayi alkawarin aiki don zaman lafiya da cigaban Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace zai ci gaba da aiki ba ji ba gani domin cigaban zaman lafiyam kare al’umma da kuma inganta Najeriya, ba tare da la’akari da tushe ko wariya a tsakanin al’umman kasar ba.

Shugaban kasar ya bayar da tabbacin ne a jawabinsa na kasa baki daya domin murnar cikar Najeriya shekaru 58 da samun yancin kai a Abuja, a ranar Litinin, 1 ga watan Oktoba, kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito.

Legit.ng ta tattaro cewa Shugaba Buhari ya bukaci dukkanin al’umman kasar Najeriya da su ci gaba da inganta martaba da hadin kan kasar maimakon yi abubuwan da ka iya haddasa rabuwar kai.

Ranar yanci: Buhari yayi alkawarin aiki don zaman lafiya da cigaban Najeriya

Ranar yanci: Buhari yayi alkawarin aiki don zaman lafiya da cigaban Najeriya
Source: Depositphotos

Shugaba Buhari ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatinsa zata ci gaba da tallafawa duk shirye-shiryen da zai magance matsalolin wannan lokaci.

Yace wadannan matsalli sun hada da rikice-rikicen duniya da na yanki, ta’addanci, laifuka, sauyin yanayi, yancn dan adam, daidaito tsakanin jinsi, ci gaba, talauci, da kuma rashin adalci a tsakanin kasshe da dai sauransu.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kai mamaya ofishin yan sanda a Delta, sun kashe jami’ai 2 sannan sun kwashe makamai

A matakin kasa da kasa, Shugaba Buhari yace Najeriya zata ci gaba da kasancewa mai da’a da mutunta kasashen duniya.

Kan ci gaban damokradiya da al’adar kasar,shugaban kasar ya lamunce cewa lamarin ba mai sauki bane.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel