Rikicin siyasar Kano ya dauki sabon salo yayin da PDP zata fitar da takarar gwamna a yau

Rikicin siyasar Kano ya dauki sabon salo yayin da PDP zata fitar da takarar gwamna a yau

Uwar jam’iyyar PDP ta kasa ta umarci shugabancin jam’iyyar PDP reshen jahar Kano data shirya zaben fitar da gwanin da zai tsaya mata takarar gwamnan jahar Kano a zaben 2019 a ranar Litinin, 1 ga watan Oktoba, inji rahoton Daily Nigerian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban riko na jam’iyyar PDP, Rabiu Suleiman Bichi ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, 30 ga watan Satumba, inda yace uwar jam’iyyar ce ta kasa ta basu wannan umarni, ya kara da cewa zasu gudanar da zaben a marhaba silma.

KU KARANTA: Ribadu ya janye daga zaben fidda gwani na gwamnan APC a Adamawa ya kafa hujja

Idan zaa’ tuna a ranar Lahadi ya kamata a gudanar da wannan zabe kamar yadda aka yi a jihohi da dama, sai dai tsoron abinda ka je ka dawo ya sanya jam’iyyar dage zaben, don haka yayan jam’iyyar sun saki jiki sai kwatsam ga wannan umarni ya zo.

Jam’iyyar ta daura nauyin shugabantar wannan zabe a hannun wani tsohon karamin ministan harkokin kasashen waje, Dubem Onyia, amma fa yawancin yan takarar gwamnan da ma shuwagabannin jam’iyyar basu da masaniya game da hakan.

Babbar matsalar da zaben zai iya fuskanta itace a yanzu haka akwai hukuncin kotu da ta haramta shugabancin jam’iyyar PDP a karkashin ikon Rabiu Suleiman Bichi, na hannun daman Kwankwaso, haka zalika babu tabbacin adadin wakilan da zasu kada kuri’unsu.

Daga cikin wadanda ake sa ran zasu fafata a wannan zaben kwai Abba K Yusuf, Jafar Sani Bello, Sadiq Wali, Abrahim Al-Amin Little, Hafiz Abubakar, Aminu Dabo da Salihu Sagir Takai.

A wani labarin kuma tun a ranar Asabar 29 ga watan Satumba ne dai Yansandan Najeriya suka mamaye wajen da jam’iyyar PDP ke kokarin shirya zabe a Kano, Marhaba Silma, sai dai wasu na ganin hakan nada nasaba da haramcin da kotu ta daura akan shugabancin PDP mai ci a Kano.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel