Yan bindiga sun kai mamaya ofishin yan sanda a Delta, sun kashe jami’ai 2 sannan sun kwashe makamai

Yan bindiga sun kai mamaya ofishin yan sanda a Delta, sun kashe jami’ai 2 sannan sun kwashe makamai

- Yan bindiga sun kai hari ofishin yan sanda na Aboh a karamar hukumar Ndokwa ta gabas dake jihar Delta

- An kashe jami'an yan sanda biyu a harin yayinda wasu suka ji rauni

- Yan bindigar sun kuma tsere da makamai daga ofishin yan sandan

Wasu yan bindiga rufe da fuska sun kai hari ofishin yan sanda na Aboh a karamar hukumar Ndokwa ta gabas dake jihar Delta, sun kashe jami’ai biyu sannan suka gudu da muggan makamai a safiyar ranar Asabaa, 29 ga watan Satumba.

A cewar majiyoyi, yan bindigan sun isa garin sannan suka bude wuta akan jami’an yan sandan dake baki aiki a ofishinsu, inda suka kashe mutun biyu sannan suka raunata wasu da dama kafin suka tsere da makamai.

Yan bindiga sun kai mamaya ofishin yan sanda a Delta, sun kashe jami’ai 2 sannan sun kwashe makamai

Yan bindiga sun kai mamaya ofishin yan sanda a Delta, sun kashe jami’ai 2 sannan sun kwashe makamai
Source: Depositphotos

Wata majiya wacce tayi Magana da jaridar The Punch tace: “Yan fashin sun farma yan sanda ne cikin bazata. Sun kai hari ofishin yan sandan sannan suka kashe jami’ai biyu sannan mutun daya ya tsere da raunukan alburushi.

“Daya daga cikin jami’an yan sandan ya mutu anan take sannan dayan ya mutu a hanyar zuwa asibiti, yayinda wanda ya samu rauni ke karban maganai a wani asibiti.

“Sun kuma tsere da makamai a ofishin yan sandan. Rigan jami’ar yan sanda, wacce ke a bakin kofar shiga ofishin, a tsere ba tare da raunin komai ba bayan ta fadama yan bindigan cewa ita yar gudun hijira da ambalyar ruwa ya afka mawa ne."

KU KARANTA KUMA: Tsohon shugaban EFCC Ribadu ya janye daga zaben fidda gwani na gwamnan APC a Adamawa ya kafa hujja

Wata majiya ta yan sanda wacce ta kuma tabbatar da harin, tace maharan sun tsere da injin jirgin ruwa na sintiri wacce mallakar yan sandan ruwa ne a aka tura garin.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa wasu 'yan bindiga a ranar Lahadi sun tare motoci biyar tare da sace dukkan mutanen dake ciki a kauyen Tashar Tsuntsaye dake a kusa da Kiriga, karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Kakakin yan sandan jihar Delta, Andrew Aniamaka ya tabbatar da lamarin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel