Yanzu-Yanzu: Wasu 'yan bindiga sun sace motoci 5 makare da mutane a Kaduna

Yanzu-Yanzu: Wasu 'yan bindiga sun sace motoci 5 makare da mutane a Kaduna

- Wasu 'yan bindiga sun sace motoci 5 makare da mutane a Kaduna

- A kauyen Tashar Tsuntsaye dake a kusa da Kiriga aka sace su

- Yan sanda sun tabbatar da faruwar hakan

Wasu 'yan bindiga a ranar Lahadi sun tare motoci biyar tare da sace dukkan mutanen dake ciki a kauyen Tashar Tsuntsaye dake a kusa da Kiriga, karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Yanzu-Yanzu: Wasu 'yan bindiga sun sace motoci 5 makare da mutane a Kaduna

Yanzu-Yanzu: Wasu 'yan bindiga sun sace motoci 5 makare da mutane a Kaduna
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Wani dattijon Arewa yayi wa Buhari kaca-kaca

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar da shugaban kungiyar dake rajin kare muradun 'yan garin na Birnin Gwari din watau Birnin-Gwari Vanguard for Security and Good Governance a turance, mai suna Ibrahim Nagwari.

Legit.ng ta samu haka zalika cewa mutanen da aka sace suna cikin wata motar haya ce kirar Golf da kuma wasu manyan motoci hudu.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Najeriya shiyyar Kaduna, Yakubu Sabo ya tabbatar da aukuwar hakan inda kuma ya bayyana cewa tuni jami'an su sun bazama neman barayin mutanen.

A wani labarin kuma, Daya daga cikin shugabannin kungiyar tuntuba ta dattawan Arewa a mataki na tarayya mai suna Mohammed Abdulrahman a cikin wata fira da yayi da wakilin jaridar Punch ya bayyana cewa shugaba Buhari yana nuna son kai da kabilanci a mulkin sa.

Mohammed din dai ya bayyana rashin gamsuwa da yadda shugaban kasar yake yin nade-naden sa musamman ma a bangaren tsaron kasar nan inda ya ce abin a duba ne ga dukkan mai hankali.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel