Ambode ya tona asirin dan takarar da Tinubu ke goyon baya a Legas

Ambode ya tona asirin dan takarar da Tinubu ke goyon baya a Legas

- A yayin da zaben shekarar 2019 ke kara matsowa, dangantaka tsakanin gwamna Ambode da jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, na kara lalacewa

- A yau, Lahadi, ne gwamna Ambode ya yi taro da manema labarai na kasa da kasa bayan mafi rinjayen ‘yan majalisar jihar Legas sun juya masa baya

- Yayin ganawar tasa da manema labaran, gwamna Ambode ya bayyana yadda aka taba kama dan takarar Tinubu a kasar Amurka saboda laifin damfara

A jiya ne 'yan majalisar jihar Legas suka juya wa gwamna Akinwumi Ambode baya yayin da 36 cikin 40 na mambobin suka marawa Babajide Sanwo-Olu baya a matsayin dan takarar gwamnan jam'iyyar APC a zaben 2019.

'Yan majalisan sun bayyana matsayansu ne bayan wata taro da su kayi a jiya, Asabar, karkashin jagorancin kakakin majalisar dokokin jihar Legas, Mudashiru Obasa, inda dukkan 'yan majalisar suka sanya hannu a takarda.

Ambode ya tona asirin dan takarar da Tinubu ke goyon baya a Legas

Ambode da Tinubu
Source: Depositphotos

A yau, Lahadi, ne kuma gwamnan jihar ta Legas, Akinwunmi Ambode, ya kira wani taro na manema labarai na kasa da kasa domin bayyana wasu batutuwa da suka shafi dambaruwar siyasa dake faruwa tsakaninsa da tsohon gwamna Tinubu.

DUBA WANNAN: APC ta daga zaben fitar da dan takarar gwamnan a jihohi 2, ta bayar da dalili

Yayin ganawar, gwamnan ya bayyana cewar an taba kama Sanwo-Olu, dan takarar da Tinubu ke burin tsayarwa don maye gurbin Ambode da laifin zamba a kasar Amurka.

Ambode ya bayyana cewar ba boyayyen sirri bane cewar an taba kama Sanwo-Olu da laifin buga wa tare da kasha kudin jabu a kasar Amurka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel