'Yan sanda sun hana 'yan PDP taro a Kano

'Yan sanda sun hana 'yan PDP taro a Kano

A yau, Lahadi ne jami'an 'yan sandan Najeriya suka mamaye Marhaba Cinema da ke kusa da Farm Centre a Kano bayan sun samu labarin cewa 'yan jam'iyyar PDP na jihar za su gudanar da taron a wajen.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ta ruwaito cewa 'yan sandan sun isa wajen misalin karfe 8 na safiyar yau domin su hana mutane shiga dakin taron.

'Yan sanda sun hana 'yan PDP taro a Kano

'Yan sanda sun hana 'yan PDP taro a Kano
Source: UGC

Wata kwakwarar majiya ta shaidawa NAN cewa wasu fusatattun 'yan PDP ne a jihar suka shirya taron domin tattauna matsalolin da ke afkuwa a jam'iyyar kafin a gudanar da zaben fitar da gwani na jam'iyyar.

DUBA WANNAN: Jam'iyyar PDP: Saraki ya maka Atiku da Tambuwal da kasa a zaben jin ra'ayi

Majiyar Legit.ng ta gano cewar rufe dakin taron ba zai rasa nasaba da zaben fidda gwani na gwamnoni da ake gudanarwa a jihar da kuma sauran jihohin Najeriya ba.

"An tseguntawa 'yan sanda cewar za'a gudanar da taron hakan yasa suka mamaye kofar shiga dakin taron," inji majiyar.

A lokacin rubuta wannan rahoton, 'yan sandan suna nan girke a harabar dakin taron yayin da suka yi amfani da motarsu domin toshe kofar shiga Cinemar.

Anyi kokarin tuntubar Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, Magaji Yahaya da Kwamishinan 'Yan sandan jihar, Rabiu Yusuf domin jin ta bakinsu amma wayoyinsu duk a kashe suke.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel