Yau ne Jam’iyyar APC za ta gudanar da zaben fitar da gwani a Jihohi

Yau ne Jam’iyyar APC za ta gudanar da zaben fitar da gwani a Jihohi

Yanzu haka ana can ana ta shiri inda Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya da Jihohi da dama za ta gudanar da zaben fitar da gwani na Gwamnonin Jihohi 27 kamar yadda aka tsara tun kwanaki.

Rana ba ta karya: APC za ta fitar da ‘Yan takarar da za a ba tikitin takarar Gwamna

A yau APC za ta tsaida wadanda su nemi Gwamna a 2019
Source: Twitter

A yau ne Jam’iyyar za ta fitar da wadanda za su rike mata tuta a zaben Gwamnoni da za ayi da sauran Jam’iyyu a Watan Fabrairun 2019. Za dai ayi amfani da tsarin kato-bayan-kato ne ko kuma manyan ‘Ya ‘yan Jam’iyya su tsaida ‘Yan takara.

A wasu Jihohin dai musamman inda Jam’iyyar ba ta rike da mulki ko kuma Gwamnan da ke kai yake shirin barin gado, ana neman kakaba wanda zai yi takara ne daga sama ko kuma a ware kujerar zuwa wani Yanki na Jihar da ke neman mulki.

KU KARANTA: Mataimakin shugaban kasa ya gana da babban dan hamayyar Ambode a APC

A tsarin kato-bayan-kato dai kowane ‘Dan Jam’iyya zai fito ne ya kada kuri’ar sa. A irin su Legas, Kano, Bauchi, da Zamfara za ayi amfani da irin wannan tsari. A mafi yawan Garuruwa kuma manyan ‘Ya ‘yan Jam’iyya ne za su zabi wanda za a ba tikiti.

Kawo yanzu dai ‘Yan jarida sun zura idanu su na jiran yadda za a kaya wajen fitar da ‘Yan takaran na Gwamna a Jihohi har 27 musamman a Jihohin Jam’iyyar APC da akwai ‘Yan takara masu karfi irin su Jihar Bauchi, Legas, Adamawa da dai sauran su.

Yanzu dai ba za ayi zaben a Jihohin Bayelsa, Edo, Kogi, Osun, Anambra, Ekiti da kuma Ondo ba domin wa’adin Gwamnonin da ke kan mulki bai kare ba. Haka kuma Jam’iyyar ta dage zaben Legas da Imo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel