Wainar da aka toya: Yadda tattaunawar Muhammadu Buhari da Shugaban Ghana ta kaya

Wainar da aka toya: Yadda tattaunawar Muhammadu Buhari da Shugaban Ghana ta kaya

Kwanan nan Shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya ya gana da Takwaran sa na Kasar Ghana Nana Akufo Addo a lokacin da Shugabannin Kasashen Duniya su ka hadu a Amurka.

Wainar da aka toya: Yadda tattaunawar Muhammadu Buhari da Shugaban Ghana ta kaya

Shugaba Muhammadu Buhari tare da Nana Akufo Addo a New York
Source: Facebook

Manyan Shugabannin na Afrika sun zauna ne bayan an kammala wani taro na Majalisar Dinkin Duniya da aka yi a Garin New York na Kasar Amurka. Shugaba Buhari ya gana shi-kadai da Shugaban Kasar Ghana da na Afrika ta Kudu.

Shugaba Buhari yayi wa Nana Addo magana ne kan batun ‘Yan Najeriya da ake kokarin fatattakowa daga Kasar Ghana a dawo da su gida. Shugaban na Ghana ya tabbatarwa Muhammadu Buhari na Najeriya cewa ba haka abin yake ba.

KU KARANTA: Shugaba Buhari da Matar sa sun iso Najeriya lafiya

Shugaba Nana Akufo Addo ya fadawa Shugaban kasar Najeriya Buhari cewa Gwamnatin sa ba ta harin ‘Yan Najeriya kamar yadda ake kokarin rayawa inda ya tabbatar da cewa Najeriya da Kasar Ghana za su cigaba da samun kyakkyawar alaka.

Muhammadu Buhari dai ya bayyana wannan ne a shafin sa na Tuwita bayan sun gama tattaunawa da Takwaran na sa na sa na kasar Ghana. Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa kasashen za su cigaba da rike juna da martabar da ya kamata.

Shugaban na Najeriya dai ya gana da Shugabannin Duniya inda har ya zauna da Shugaban Kungiyar OIC ta Musulunci bayan ya gabatar da jawabin sa a gaban sauran Shugabannin kasashe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel