Da dumin sa: Shugaba Muhammadu Buhari da uwar gidan sa sun dawo Najeriya

Da dumin sa: Shugaba Muhammadu Buhari da uwar gidan sa sun dawo Najeriya

- Shugaba Muhammadu Buhari da uwar gidan sa sun dawo Najeriya

- Shugaban ya dawo ne cikin dare

- Shugaba Buhari dai yaje kasar Amurka ne

Labarin da muka samu daga majiyoyin mu sun tabbatar mana da cewa Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari tare da uwar gidan sa da sauran 'yan tawagar sa sun iso gida Najeriya bayan shafe kwanaki suna wata ziyarar aiki a birnin New York na kasar Amurka.

Da dumin sa: Shugaba Muhammadu Buhari da uwar gidan sa sun dawo Najeriya

Da dumin sa: Shugaba Muhammadu Buhari da uwar gidan sa sun dawo Najeriya
Source: Facebook

Kamar dai yadda muka samu, shugaban kasar tare da 'yan tawagar ta sa sun iso a filin sauka da tashi na jiragen sama na kasa da kasa na tunawa da Nnamdi Azikwe dake garin Abuja, babban birnin tarayya da daren ranar Lahadi.

Mai karatu dai in bai manta ba shugaban kasar ya je kasar Amurka din ne inda ya halarci taron shugabannin kasashen duniya na shekara shekara da majalisar dinkin duniya ke shiryawa.

Da dumin sa: Shugaba Muhammadu Buhari da uwar gidan sa sun dawo Najeriya

Da dumin sa: Shugaba Muhammadu Buhari da uwar gidan sa sun dawo Najeriya
Source: Facebook

Da dumin sa: Shugaba Muhammadu Buhari da uwar gidan sa sun dawo Najeriya

Da dumin sa: Shugaba Muhammadu Buhari da uwar gidan sa sun dawo Najeriya
Source: Facebook

A wani labarin kuma, Daya daga cikin shugabannin kungiyar tuntuba ta dattawan Arewa a mataki na tarayya mai suna Mohammed Abdulrahman a cikin wata fira da yayi da wakilin jaridar Punch ya bayyana cewa shugaba Buhari yana nuna son kai da kabilanci a mulkin sa.

Mohammed din dai ya bayyana rashin gamsuwa da yadda shugaban kasar yake yin nade-naden sa musamman ma a bangaren tsaron kasar nan inda ya ce abin a duba ne ga dukkan mai hankali.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel