Zaben Osun: Jam'iyyar PDP ta saki jerin sunayen mambobin ta da aka kashe

Zaben Osun: Jam'iyyar PDP ta saki jerin sunayen mambobin ta da aka kashe

- Jam'iyyar PDP ta ce zata saki jerin sunayen mambobin ta da aka kashe

- Tace an murde mata zaben jihar Osun amma ita taci

- Tuni har ta garzaya kotu

Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya shiyyar jihar Osun dake a kudu maso yammacin kasar nan a ta bakin shugaban ta Mista Soji Adagunodo ta bayyana cewa yanzu haka ta yi nisa wajen tattara sunayen mambobin ta da suka mutu a zaben gwamnan jihar da ya gabata.

Zaben Osun: Jam'iyyar PDP ta saki jerin sunayen mambobin ta da aka kashe

Zaben Osun: Jam'iyyar PDP ta saki jerin sunayen mambobin ta da aka kashe
Source: Original

KU KARANTA: Yan Boko Haram sun fara kashe kan su da kansu

Mista Soji wanda yace tuni uwar jam'iyyar a jiha ta aike da bukatar kiran dukkan shugabannin ta a matakin kananan hukumomi da kuma mazabu domin tattara sunayen da tace kuma zata sake su ta hanyar wallafawa duk duniya ta gani.

Legit.ng dai ta samu cewa jam'iyyar APC mai mulki ce ta lashe zaben na jihar Osun bayan zagaye na biyu na zaben da aka gudanar a wasu mazabun da akayi rikici a zaben.

Tuni dai jam'iyyar PDP ta yi fatali da sakamakon zaben tare kuma da garzayawa kotu domin bin kadin lamarin.

A wani labarin kuma, Daya daga cikin shugabannin kungiyar tuntuba ta dattawan Arewa a mataki na tarayya mai suna Mohammed Abdulrahman a cikin wata fira da yayi da wakilin jaridar Punch ya bayyana cewa shugaba Buhari yana nuna son kai da kabilanci a mulkin sa.

Mohammed din dai ya bayyana rashin gamsuwa da yadda shugaban kasar yake yin nade-naden sa musamman ma a bangaren tsaron kasar nan inda ya ce abin a duba ne ga dukkan mai hankali.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel