Zaben fidda gwani: Fadar shugaban kasa tayi tsokaci kan nasarar da Buhari ya samu

Zaben fidda gwani: Fadar shugaban kasa tayi tsokaci kan nasarar da Buhari ya samu

- A ranar Juma'a 28 ne APC ta gudanar da zaben fidda gwani na shugabancin kasa a dukkan jihohin Najeriya

- Sakamakon zabukkan da aka samu a jihohi daban-daban ya nuna cewa miliyoyin 'yan jam'iyyar APC na goyon bayan tazarcen shugaba Buhari

- Fadar Shugaban kasa tayi alfahari da wannan sakamakon inda ta ce alama ce da ke nuna za'a samu nasara a zaben 2019

Fadar shugban kasa ta ce nasarar da shugaba Buhari a ya samu a zaben fidda gwani da a kayi ranar Juma'a a jihohin Najeriya inda aka zabi Buhari a matsayin dan takarar shugabancin kasa tilo na jam'iyyar APC alamar nasara ne a zaben na 2019.

Zaben fidda gwani: Fadar shugaban kasa tayi tsokaci kan nasarar ba Buhari ya samu

Zaben fidda gwani: Fadar shugaban kasa tayi tsokaci kan nasarar ba Buhari ya samu
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: PDP ta bani cin hancin makudan miliyoyi don na bar APC - Sanatar Arewa

A sanarwar da ta fito daga bakin babban mai taimakawa shugaban kasa, Garba Shehu a ranar Asabar, ya ce miliyoyin 'yan jam'iyya da suka fito kwansu da kwarkwata domin jefawa shugaban kasa kuri'a na nuna cewa har yanzu Buhari yana da farin jini wajen mutane.

"Baya ga cewa wannan nasara ce ga shugaban kasa da jam'iyyar APC, nasarar kanta sako ce ga 'yan siyasa cewa kawo ayyukan cigaba da mulki mai inganci ya fi muhimmanci da siyasar raba kawunan al'umma'

"Darasin da da wasu sauran jam'iyyu za su iya koya itace ya kamata su fara koyi da tsarin shugabancin Muhammadu Buhari.

"Muna kuma mika godiyar mu ga dukkan wadanda suka taimaka wajen ganin an samu wannan gagarumin nasarar," inji Garba Shehu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel