Karin bala'i ga Ambode yayin da mataimakin shugaban kasa ya gana da babban dan hamayyar sa

Karin bala'i ga Ambode yayin da mataimakin shugaban kasa ya gana da babban dan hamayyar sa

- Gwamnan Legas, Akinwumi Ambode ya sake shiga wata cakwakiyar

- Osinbajo ya gana da babban dan hamayyar sa

- Ambode dai yana funskantar barazanar faduwa zaben fitar da gwani

Yayin da lamurra ke cigaba da kwancewa gwamnan jihar Legas, Mista Akinwumi Ambode game da kalubalen da yake fuskanta a siyasar jihar ta Legas, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya gaba da babban dan hamayyar sa, Babajide Sanwo-Olu.

Karin bala'i ga Ambode yayin da mataimakin shugaban kasa ya gana da babban dan hamayyar sa

Karin bala'i ga Ambode yayin da mataimakin shugaban kasa ya gana da babban dan hamayyar sa
Source: Facebook

KU KARANTA: Jami'an tsaron Najeriya sun gano dumbin kudade a wani kango

Farfesa Osinbajo din dai ya gana da Babajide Sanwo-Olu ne tare kuma da dayan mai neman tikitin takarar gwamnan jihar a jam'iyyar APC, Dakta Femi Hamzat wanda daga baya ya janye ya bar wa shi Babajide Sanwo-Olu din.

Legit.ng dai ta samu cewa Gwamnan na jihar Legas, Akinwumi Ambode dai ya dan samu sabani da jigon jam'iyyar ta APC CIf Bola Tinubu wanda kuma yanzu haka ake zargin shi ne ke da hannu cikin fitowa Babajide Sanwo-Olu din domin ya kada Ambode.

A wani labarin kuma, Daya daga cikin masu neman tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa labaran da ake yadawa na cewa bai ji dadin kai zaben fitar da gwanin su ba a garin Fatakwal ba gaskiya bane.

Atiku wanda yace shi garin Fatakwal kusan gida ne a gare shi ya bayyana cewa baya ma bukatar masauki ko wani tsaro na musamman domin kuwa a yi wani bangare na rayuwar sa a garin a shekarun baya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel