2019: Mutanen Kudu za su fito kwan su da kwarkwata su zabi Buhari – Rochas Okorocha

2019: Mutanen Kudu za su fito kwan su da kwarkwata su zabi Buhari – Rochas Okorocha

A kwanan nan ne mu ka samu labarin abin da Jam’yyar adawa ta PDP ta rika yi wa Shugaba Muhammadu Buhari a zabukan baya a Kasar Inyamurai daga bakin Gwamnan Imo Rochas Okorocha.

2019: Mutanen Kudu za su fito kwan su da kwarkwata su zabi Buhari – Rochas Okorocha

Buhari zai lashe zabe a 2019 – Inji Gwamnan Imo
Source: Facebook

Gwamna Rochas Okorocha yayi wani jawabi a karshen makon nan a wani katafaren hotel a Jihar Imo bayan an sanar da sakamakon zaben APC na Shugaba Buhari wanda shi ne tilon ‘Dan takarar Jam’iyyar a zaben 2019.

Rochas Owelle Okorocha yace a 2015 ba wai Mutanen Ibo ba su zabi Shugaba Buhari ba ne sai dai an murde zaben ne da karfin tsiya. Gwamnan yace Jam’iyyar PDP tayi coge ne a zaben domin hana Muhammadu Buhari kai labari.

KU KARANTA: PDP ta ban makudan kudi domin in rabu da APC

Gwamnan wanda yake shirin ajiye mulki ya bayyana cewa Shugaba Buhari zai lashe zabe a kasar Inyamurai a zaben 2019. Gwamnan yace a 2019 dai shi da Mutanen Jihar Imo su na tare da Shugaba Buhari a zaben na 2019.

Okorocha wanda yayi takarar Shugaban kasa da Buhari a Jam’iyyar APC a 2014 yake cewa Jam’iyyar PDP ta kan kawo kuri’un karya ne kurum da aka rubuta a daki a matsayin sakamakon zabe domin takawa Buhari burki.

Gwamnan na Imo Mai Girma Rochas Owelle Okorocha yace coge aka rika yi a 2011 da ma zaben 2015 amma Shugaba Buhari zai yi nasara a zaben 2019 domin Inyamurai ba su da wanda za su zaba da zai fi shi a badi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel