Maganar cewa na fasa takara kanzon kurege ne – Inji Ribadu

Maganar cewa na fasa takara kanzon kurege ne – Inji Ribadu

Labari ya zo mana cewa tsohon Shugaban Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin azrikin kasa zagon-kwasa Nuhu Ribadu ya karyata maganar cewa an yi masa alkawarin kujerar Minista.

Maganar cewa na fasa takara kanzon kurege ne – Inji Ribadu

Ribadu yace babu maganar janye takarar Gwamna a Adamawa
Source: Depositphotos

Ana ta rade-radin cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai nada Nuhu Ribadu Minista idan har ya janyewa Dr. Mahmud Haliluu Ahmed takarar sa a Adamawa. Mahmood Halilu dai Suruki ne wajen Shugaban kasa Buhari.

Ribadu ya musanya wannan batu jiya inda yace babu wani alkawarin Minista da aka yi masa a Najeriya. Shugaban Hukumar na EFCC na farko ya karyata wannan magana ne ta shafin sa na sadarwa na zamani na Tuwita.

KU KARANTA: Bukola Saraki ya tika su Atiku da kasa a wani zaben gwaji

Nuhu Ribadu ya nuna cewa bai janye daga takarar Gwamnan da yake shirin yi ba inda ake tunani zai kara da Gwamna mai-ci Jibrilla Bindow da kuma shi Surukin na Shugaba Buhari wajen samun tikitin Jam’iyyar APC.

Darektan yakin neman zaben ‘Dan takarar Gwamnan dai ya karyata cewa Ribadu ya janye takarar sa inda ya nuna cewa Ribadu bai da niyyar yi wa Gwamna mai-ci Jibril Bindow taron dangi da Mahmud Halilu.

Jiya kun ji cewa Gwamnan Adamawa Jibrilla Bindow yana cikin wadanda sai yayi da gaske wajen samun tikitin APC a zaben fitar da gwani da za ayi. Surukin na Shugaba Buhari yana da goyon bayan sauran manyan APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel