Sabon salo: Jam’iyyar KOWA ta yiwa ‘yan takararta na shugaban kasa jarrabawa

Sabon salo: Jam’iyyar KOWA ta yiwa ‘yan takararta na shugaban kasa jarrabawa

- Jam’iyyar KOWA ta amince da tsarin yin zabe ta yanar gizo da rubuta jarrabawa ga masu burin yin takara a karkashin inuwar jam’iyyar

- Abimbola Oyedokun, shugaban jam’iyyar KOWA na kasa ne ya sanar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a Legas

- Mista Ayedokun ya shaidawa NAN cewar yanzu haka jam’iyyar KOWA na da ‘yan takarar shugaban kasa guda 3

A yau, Asabar, ne jam’iyyar KOWA ta amince da tsarin yin zabe ta yanar gizo da rubuta jarrabawa ga masu burin yin takara a karkashin inuwar jam’iyyar.

Abimbola Oyedokun, shugaban jam’iyyar KOWA na kasa ne ya sanar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a Legas.

Mista Ayedokun ya nemi hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta gudanar zabukan shekarar 2019 ta hanyar zaben yanar gizo domin samun sakamakon zabe sahihi da babu magudi a cikinsa.

Sabon salo: Jam’iyyar KOWA ta yiwa ‘yan takararta na shugaban kasa jarrabawa

Shugabannin Jam’iyyar KOWA
Source: Twitter

Dalilin da yasa ake samun magudi a zaben Najeriya shine hukumar INEC ta kit a rungumi tsari na zamani, na gudanar da zabe ta hanyar amfani da na’ura mai kwakwalwa da aka hada da yanar gizo.

Da hukumar INEC tayi riko da irin wannan tsari da ba za a ke samun matsalar maimaita zabe ko dammar yin magudi ba. Mu yanzu a KOWA wakilai zasu gudanar da zabe ne ta na’ura mai kwakwalwa, zasu fara zabe daga karfe 8:00 na safe zuwa karfe 2:00 na rana. Abu ne mai sauki,” a cewar Misata Ayedokun.

DUBA WANNAN: APC ta daga zaben fitar da dan takarar gwamna a jihohi 2, ta fadi dalili

Mista Ayedokun ya shaidawa NAN cewar yanzu haka jam’iyyar KOWA na da ‘yan takarar shugaban kasa guda 3, biyu daga jihar Legas; Sina Fagbenro-Byron da Ayobo Lijadu.

Sannan ya kara da cewa ‘yar takara tau kun ita ce Farfesa Remi Sonaiya, wacce ta yiwa jam’iyyar KOWA takarar shugaban kasa a shekarar 2015.

A cewar sa, ‘yan takarar shugaban kasa a jam’iyyar sun rubuta jarrabawa a jiya, Juma’a, domin gwada basirarsu da kuma fahimtar su a kan matsalolin dake damun Najeriya da kuma hanyoyin da suke ganin zasu bi domin warware matsalolin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel