Mata ta da Buhari ne kadai masu gidana a duniya - gwamnan PDP

Mata ta da Buhari ne kadai masu gidana a duniya - gwamnan PDP

Gwamna David Umahi na Jihar Ebonyi ya ce bayan mai dakinsa, shugaba Muhammadu Buhari abokinsa ne kuma shine kadai mai gidansa.

Gwamnan ya ce ya kamata dukkan 'yan Najeriya su rika girmama shugaba Muhammadu Buhari saboda daraja da matsayin kujerarsa ta shugabancin kasa.

Ya ce baya jin kunyar bayyana cewa Shugaba Buhari abokinsa ne duk da cewa shi dan jam'iyyar adawa ta PDP ne.

Bayan mai dakina, Buhari ne mutumin da nafi darajawa - Gwamnan PDP

Bayan mai dakina, Buhari ne mutumin da nafi darajawa - Gwamnan PDP

DUBA WANNAN: An kwance wa gwamnan Legas zani a kasuwa, dukkan yan majalisar jihar basu yinsa

"Buhari a matsayinsa na shugaba wakili ne na Najeriya kamar yadda gwamnoni suke matsayin kananan shugabanin kasashe a jihohinsu.

"Shugaba Buhari dan adam ne kuma akwai yiwuwar ya aikata kuskure amma addu'a ta shiriya ya kamata ayi masa domin ya jagoranci Najeriya kan tafarkin da ya dace.

"Kamar yadda na maimaita a baya, ba zan zage shugaban kasa ba domin nuna cewa ni dan PDP ne domin ba shine aiki na a matsayin gwamna ba," inji Umahi.

Ya kara da cewa abokatar da shugaba Buhari ba ta nuna cewa jama'ar Ebonyi za su zabi APC, ya ce jam'iyyar ta PDP ne kuma zai yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da cewa ba'a kwace jihar daga hannunsu ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel