Da duminsa: Jam’iyyar APC ta daga zaben fitar da dan takarar gwamna a jihohi 2

Da duminsa: Jam’iyyar APC ta daga zaben fitar da dan takarar gwamna a jihohi 2

Uwar jam’iyyar APC ta kasa ta sanar da daga zaben fitar dad an takarar gwamna a jihohin Legas da Imo.

Jam’iyyar ta daga zaben jihohin ne saboda matsalar kai kayan aiki zuwa jihohin, kamar yadda shuigaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole, ya sanar.

A jiya ne jam’iyyar APC mai mulki ta gudanar da zaben tabbatar da shugaba Buhari a matsayin dan takararta na shugaban kasa a zaben shekarar 2019.

Kamar yadda jam’iyya ta bayyana a baya, ta gudanar da zaben shugaban Buhari kai tsaye, ma’ana kato bayan kato.

Da duminsa: Jam’iyyar APC ta daga zaben fitar da dan takarar gwamna a jihohi 2

Jam’iyyar APC ta daga zaben fitar da dan takarar gwamna a jihohi 2
Source: Depositphotos

Duk da kasancewarsa dan takarar daya tilo daya sayi fam din takarar shugaban kasa a APC, jam’iyyar ta ce sai ta gudanar da zabukan tabbatar da shi a fadin jihohin kasar nan domin yin biyayya ga siyasa da kuma nunawa duniya farin jinin da shugaban keda shi har yanzu a tsakanin mambobin jam’iyyar APC.

DUBA WANNAN: Zaben cikin gida: Sakamakon zaben Buhari daga jihohi 5

Da yake sanar da sakamakon zaben jiya a Kano, gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewar shugaba Buhari ya sanu adadin kuri’u 2,931,235 daga ‘yan jam’iyyar APC dake fadin kananan hukumomi 44 a jihar Kano.

Tun da fari jam’iyyar APC ta amince cewar gwamnonin jihohin da take mulki ne zasu kasance manyan jami’an zaben cikin gidan na jiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel