Zaben Osun: Abinda muka yi wa Omisore alkawari a APC - Oshiomhole

Zaben Osun: Abinda muka yi wa Omisore alkawari a APC - Oshiomhole

- An gwabza tsakanin APC da PDP a Osun a makon jiya

- Anyi kan-kankan a zagayen farko, sai dai APC ta kwace tafiyar a zagaye na biyu

- APC ta mazge PDP ne bayan ta lasa wa SDP alawa a baka

Zaben Osun: Abinda muka yi wa Omisore alkawari a APC - Oshiomhole

Zaben Osun: Abinda muka yi wa Omisore alkawari a APC - Oshiomhole

Adams Oshiomhole, shugaban jam'iyyar APC, ya tabbatar wa manema labarai cewa, jam'iyyarsa ta APC ta shiga kawance da takwararsu ta SDP ta Abiola a zaben OSun, inda suka tattauna da Sanata Iyiola Omisore wanda yazo na uku a zaben.

An dai dauka ko kujerar Sanata ko Minista shugaban na APC yayi masa alkawari, amma Adams yace sam ba wannan magana.

A cewarsa, sun dai tattauna yadda zasu hada kai don ci gaban jiihar ta fannin ilimi, samar da ayyukan yi, da ma yadda zasu iya cin zabe a jihar a zaben shugaban kasa mai zuwa a badi.

DUBA WANNAN: Sai na zarce zaku san me ake kira aiki - Buhari

A cewar Oshiomole dai, kar a manta, Iyiola Omisore, ya taba yin mataimakin gwamna a jihar karkashin Bisi Akande, wanda yanzu jigo ne a APC, kuma ya taba shugabantar APC din bayan da aka samar da ita.

Watakil dai, minista zasu yi masa bayan an zarce a Abuja, bai fito ya fadi ba, duk da dai hakan ake sa rai.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel