An kwance wa gwamnan Legas zani a kasuwa, dukkan yan majalisar jihar basu yinsa

An kwance wa gwamnan Legas zani a kasuwa, dukkan yan majalisar jihar basu yinsa

'Yan majalisar jihar Legas sun juya wa gwamna Akinwumi Ambode baya yayin da 36 cikin 40 na mambobin suka marawa Babajide Sanwo-Olu baya a matsayin dan takarar gwamnan jam'iyyar a zaben 2019.

'Yan majalisan sun bayyana matsayansu ne bayan wata taro da su kayi a yau Asabar karkashin jagorancin Kakakin majalisar jihar, Mudashiru Obasa inda dukkan 'yan majalisar suka sanya hannu a takarda.

An kwance wa gwamnan Legas zane a kasuwa, dukkan yan majalisar jihar basu yinsa

An kwance wa gwamnan Legas zane a kasuwa, dukkan yan majalisar jihar basu yinsa
Source: Twitter

Sanarwan ta fito ne daga ciyaman din kwamitin sadarwa da tsare-tsare da tsaro na majalisar, Mr Adefunmilayo Tejuoso inda ya bayyana cewa sun dauki matakin ne bayan taron da suka gudanar ranar Asabar.

DUBA WANNAN: Abin boye ya fito: Sirrukan sabon gwamnan Osun, Oyetola, da baku sani ba

Kazalika, daya daga cikin masu neman takarar gwamna jihar Legas karkashin jam'iyyar APC, Obafemi Hamzat shima ya janye takararsa tare da marawa Sanwo-Olu baya.

Hamzat ya umurci dukkan magoya bayansu su marawa Sanwo-Olu baya a zaben fitar da gwani da za'a gudanar a jihar.

A halin yanzu Sanwo-Olu shine dan takarar da zai fafata da gwamna Akinwunmi Ambode wanda aka hasashen jigo a jam'iyyar ta APC, Cif Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ne mai gidansa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel