Raba gardama: Oshiomhole ya yi subutar baki yayin kare APC a kan zargin magudi a zaben Osun

Raba gardama: Oshiomhole ya yi subutar baki yayin kare APC a kan zargin magudi a zaben Osun

A ranar Alhamis, 27 ga watan Satumba, ne jama’ar jihar Osun daga kananan hukumomin Ife ta kudu, Ife ta arewa, Olorun da Osogbo suka fita filin zabe domin kada kuri’a a zaben raba gardama tsakanin dan takarar gwamna a jam’iyyar APC, Gboyea Oyetola, da takwaransa na PDP, Ademola Adeleke.

Jam’iyyar PDP da dan takarar ta sun koka kan cewar an yi masu magudi a zaben tare da yin kira ga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta rushe zaben raba gardamar ta kuma bayyana Adeleke a matsayin sabon gwamnan jihar Osun tunda shine ya yi nasara a zagaye na farko na zaben.

Sai dai a wata hira da aka yi da shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya yi subutar baki a kokarinsa na kare jam’iyyar daga zargin tafka magudi.

Raba gardama: Oshiomhole ya yi subutar baki yayin kare APC a kan zargin magudi a zaben Osun

Oshiomhole ya yi subutar baki yayin kare APC a kan zargin magudi a zaben Osun
Source: Depositphotos

A kokarinsa na bayyana cewar babu wata matsala dangane da zaben, Oshiomhole ya amsa cewar an yi magudi a zaben kafin daga baya ya gaggauta janye Kalmar da ya yi amfani da ita.

DUBA WANNAN: Kato bayan kato: Ganduje ya bayyana adadin miliyoyin kuri'u da Buhari ya samu a Kano

Yayin da yake karyata batun yin magudin a zaben a hirarsa da gidan talabijin na Channels, Oshiomhole ya ce, “ba zamu samu cigaba a siyasa ba sai ‘yan siyasa sun zama masu hakuri yayin da aka yi masu magudin zabe,ku yi hakuri! Ina nufin idan kayar da su a zabe,” a kalaman Oshiomhole

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel