Wani 'Dan Kasar Ghana ya kashe Uwargidan sa a jihar Oyo

Wani 'Dan Kasar Ghana ya kashe Uwargidan sa a jihar Oyo

Mun samu cewa wani dan asalin kasar Ghana, Bonga Augustus, dake zaune a kauyen Baba Ijebu na garin Ibadan a jihar Oyo, ya sheke uwargidansa da kuma kansa murus har lahira da Gatari na sarar Itace.

Rahotanni kamar yadda shafin jaridar The Punch suka ruwaito, Augustus wanda dattijantaka ta cimma sa ya kuma yin amfani da Gatarin wajen raunata Agolarsa kafin ya yankewa kansa wannan mummunan hukunci.

Wannan Dattijo da ya haura shekaru 60 a doron kasa ya kashe Mai dakinsa, Margaret, 'yar asalin jihar Benuwe bayan da wata sa'insa ta shiga tsakanin su a ranar Alhamis din da ta gabata.

A yayin tatsar rahoto na manema labarai daga mazauna da kuma makwabta wannan yanki na karkara, sun bayyana cewa lamarin ya auku cikin duhu na dare inda sai karaji da kururuwa ce ta sanya suka farka daga bacci cikin razani.

Wani 'Dan Kasar Ghana ya kashe Uwargidan sa a jihar Oyo

Wani 'Dan Kasar Ghana ya kashe Uwargidan sa a jihar Oyo

Sai dai ko shakka ba bu kafin su kai wani dauki tuni 'ya'yan hanjin Marigayiya Margaret sun fito waje da nan take ta gama shure-shurenta na zafin fitar rai.

KARANTA KUMA: Sauyin yanayi ke haddasawa Matasan Najeriya ƙaura zuwa 'Kasashen Turai - Buhari

Cikin wannan yanayi marigayi Augustus ya kuma dabawa kansa sara da wannan Gatari inda aka yi gaggawar mika shi ofishin 'yan sanda na kurkusa da anan rai ya yi masa halinsa ba tare da wani ban mamaki ba.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, kakakin hukumar 'yan sanda na jihar Adekunle Ajisebutu, ya tabbatar da aukuwar wannan mummunan lamari inda ya ce tuni bincike ya kan kama domin gano ainihin ba'asi da kuma sanadiyar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel