Da dumi dumi: Dr Mimiko ya fice daga jam'iyyar Labour Party LP

Da dumi dumi: Dr Mimiko ya fice daga jam'iyyar Labour Party LP

- Tsohon gwamnan jihar Ondo, Olusegun Mimiko, ya fice daga jam'iyyar Labour Party zuwa sabuwar jam'iyyar Zenith Labour Party

- Mimiko ya yi zargin cewa shugaban ja,'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole ne ke juya jam'iyyar LP

- Tun bayan da ya bayyana kudurinsa na tsayawa takara jam'iyyar ta nisantar da kanta daga kudirinsa, hakan ya tilasta shi ficewa

Tsohon gwamnan jihar Ondo, Olusegun Mimiko, ya fice daga jam'iyyar Labour Party zuwa sabuwar jam'iyyar Zenith Labour Party. Mai magana da yawun tsohon gwamnan, Eni Akinsola, wanda ya tabbatar da sauyin shekar ya ce yanzu ya koma jam'iyyar ZLP.

A cewar Akinsola, Mimiko ya ce ya damu matuka da irin bahagon salon tafiyar jam'iyyar LP, wacce kusan ke aiki karkashin umurnin shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, wanda ya sa Mimiko tunanin APC na amfani da shuwagabannin jam'iyyar LP ne don cimma bukatunsu.

KARANTA WANNAN: APC ta bayyana dalilin da ya sa ta hana Shittu, Al-Hassan takara karkashin jam'iyyar

Akinsola ya ce: "Kwarai, ya fice daga jam'iyyar Labour Party a jiya, bayan da ya tattauna da dukkanin masu ruwa da tsaki a harkokin siyasarsa, kuma ya basu hujjojin da suka dogara akansu, dangane da irin abubuwan da ke faruwa a cikin jam'iyyar LP tun daga lokacin da ya shige ta."

Da dumi dumi: Dr Mimiko ya fice daga jam'iyyar Labour Party LP

Da dumi dumi: Dr Mimiko ya fice daga jam'iyyar Labour Party LP
Source: Depositphotos

Ya ce a ranar da Mimiko ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa, shugaban kungiyar kwadago na kasa ya ce ba sa bukatarsa a tafiyarsu, haka zalika wani mai suna Omotosho wanda ya yi ikirarin shine shugaban jam'iyyar LP a bagaren da suka rabu ya ce ba sa bukatar Mimiko a tare da su.

"Kamar yadda ake fada, wai ihu bayan hari. Rikicin shugabancin jam'iyyar PDP a wancan lokacin, ya ja har muka rasa kujerar gwamnan Ondo a 2016, wannan ita ce gaskiya. Da ace mun samu lokaci mun tsara yakin zabe kamar kowacce jam'iyya, da mun samu nasara a Ondo, amma aikin gama dai ya gama.," a cewar Akinsola.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel