APC ta bayyana dalilin da ya sa ta hana Shittu, Al-Hassan takara karkashin jam'iyyar

APC ta bayyana dalilin da ya sa ta hana Shittu, Al-Hassan takara karkashin jam'iyyar

- APC ta ce ta hana Ministan watsa labarai Adebayo Shittu tsayawa takarar gwamna saboda gazawarsa na yin NYSC

- A bangaren Jummai Al-Hassan kuwa (Mama Taraba), jam'iyyar ta hanata tsayawa takara saboda gaza yarda da biyayyarta

- Oshiomhole ya ce babu yadda za ayi mai neman takara a karkashin APC a same shi da aikata laifin sa ya sabawa dokokin jam'iyyar

A ranar Juma'a ne Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya ce jam'iyyar ta dakatar da ministan watsa labarai, Adebayo Shittu tare da takwararsa ta ma'aikatar harkokin mata, Aisha Al-Hassan daga tsayawa takara karkashin jam'iyyar don kare martabobin da jam'iyyar ta shimfida.

Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya gudanar a babban birnin tarayya Abuja a ranar Juma'a.

Oshiomhole ya ce kwamitin tantance 'yan takarar kujerar gwamna karkashin jam'iyyar ba su gamsu da bayanan da Shittu ya yi masu ba, na cewar matsayin da ya rike na majalisar dokoki a jihar Oyo da kuma ministan watsa labarai ya yi dai dai da yin bautar kasa ta NYSC.

KARANTA WANNAN: Buhari shugaban kasata ne, ba zan zage shi don banbancin jam'iyya ba - Gwamnan PDP

APC ta bayyana dalilin da ya sa ta hana Shittu, Al-Hassan takara karkashin jam'iyyar

APC ta bayyana dalilin da ya sa ta hana Shittu, Al-Hassan takara karkashin jam'iyyar
Source: Depositphotos

A cewar sa, tuni dokokin Nigeria suka warware komai dangane da batun yin NYSC. Dangane da ministar harkokin mata kuwa, Aosha Al-Hassan, ya ce an cireta ne saboda jam'iyyar bata gamsu da biyayyarta ba.

Oshiomhole ya ce: "Mun sanar da kowa dalla dalla a lokacin da guguwar sauyin sheka ta kada, cewar APC na iya amfana daga wannan sauyin shekar ma damar za ta taimaka wajen karfafa dokokin da sharudda ga duk wanda zai tsaya takara karkashin jam'iyyar, kuma babu wanda zai tsallake su.

"Dokar zabe da kuma dokar jam'iyyar APC ta haramtawa mutum daya shiga jam'iyyun siyasa sama da daya a lokaci daya. Babzai yiyu ace kana mamban APC ba sannan a ganka tare da wani a wata jam'iyyar kana nuna soyayyarka akansa, da yawansu na nuna suna tare da APC ne bayyana amma a zukatansu 'yan PDP ne."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel