Zamu ci gaba da daukar nauyin kungiyar kasashen yammacin Afirka ECOWAS - Buhari

Zamu ci gaba da daukar nauyin kungiyar kasashen yammacin Afirka ECOWAS - Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi alkawarin cigaba da ba ECOWAS tallafin kudi

- Tunda bama son muyi girman kawai, dole ne mu nemo kudi

- An bukaci taimakon shugaban kasar ne domin cigaban shirye shiryen zaben kasar Guinea-Bissau dake zuwa

Zamu ci gaba da daukar nauyin kungiyar kasashen yammacin Afirka ECOWAS - Buhari

Zamu ci gaba da daukar nauyin kungiyar kasashen yammacin Afirka ECOWAS - Buhari
Source: Facebook

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi alkawarin cigaba da ba ECOWAS tallafin kudi domin kada girma ya fadi.

Kamar yanda bayanin mataimakin shugaban kasa na musamman akan yada labarai, Mista Femi Adesina yake, Shugaban kasar yayi magana ne a matsayin shi na Chiyaman din ECOWAS a wani bayani da yayi ga shugaban kamashon ECOWAS din, Jean-Claude Brou, a New York a ranar Alhamis.

"Tunda bama son zama manyan banza, dole mu nemo kudi," inji Buhari yayin da yake alkawarin tallafin kudi ga kungiyar.

DUBA WANNAN: Dalilinmu na korar Mama Taraba - APC

An bukaci taimakon ne saboda cigaba da shirin zaben kasar Guinea-Bissau, da za'ayi nan ba da dadewa ba, Togo, inda za'ayi gyare gyare a kundin tsarin mulkin kasar tare da kasar Mali inda yanayin siyar kasar bata da kwari, duk da kammala zaben shugabancin kasar da akayi kwanan nan.

Ya umarci ministan hulda da harkokin was, Mista Geoffrey Onyeama, da ya hadu da shugaban kamashon ECOWAS domin aiki na musamman gurin samar da zaman lafiya a kasar Mali.

Buhari ya jinjiinawa aikin da ECOWAS take yi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel