2019: Kwankwaso ya roki wata alfarma daga magoya bayan Dankwambo

2019: Kwankwaso ya roki wata alfarma daga magoya bayan Dankwambo

- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya roki deleget din jihar Gombe su raba kuri'unsu tsakaninsa da Dankwambo a zaben fidda gwani da PDP

- Kwankwaso ya yi wannan rokon ne yayin da ya ziyarci Gombe domin kamfe da neman kuri'un deleget din jihar

- Kwankwaso ya kuma bukaci wakilan da su tabbatar sun zabi dan takarar da zai iya kawar da jam'iyyar APC a 2019

A jiya, Juma'a ne tsohon gwamnan Kano, Alhaji Rabiu Musa Kwankwaso ya roki deliget din jihar Gombe suyi raba dai-dai tsakaninsa da Gwamna Dankwambo idan lokacin jefa kuri'a zaben fidda gwani na takarar PDP ya yi.

Kwankwaso ya yi wannna rokon ne a ranar Juma'a 28 ga watan Satumba a Gombe, yayin da ya ziyarci mataimakin gwamnan jihar, Mr Charles Iliya.

2019: Kwankwaso ya roki wata alfarma daga magoya bayan Dankwambo

2019: Kwankwaso ya roki wata alfarma daga magoya bayan Dankwambo
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Zaben fitar da gwani: Buhari ya samu kuri'u 388,653 a jihar Rivers

Ya shaida musu cewa ya ziyarci Gombe ne domin ya sanar da su niyyarsa na fitowa takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP gabanin gudanar da zaben fidda gwanin kana ya nemi goyon bayansu.

Kwankwaso ya ce yana da kwarewar gudanar da mulki saboda ya yi gwamna sau biyu kuma gashi ya yi Sanata hakan yasa ya ke ganin zai iya ceto Najeriya daga cikin mawuyacin halin da ta shiga.

"Na san kuna da dan takara a Gombe; amma za ku iya zabansa kuma nima ku zabe ni.

"Ba zan damu ba idan kun raba kuri'un ku gida biyu kun bani rabi, shi kuma dan takarar ku ku bashi rabin," rokon Kwankwaso ga deliget din Gombe.

A jawabinsa, mataimakin gwamnan Gombe, Iliyas ya tabbatar wa Kwankwaso cewar kuri'arsu ta PDP ne kuma ya yi masa fatan alheri da takararsa na shugabancin kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel