Sauyin yanayi ke haddasawa Matasan Najeriya ƙaura zuwa 'Kasashen Turai - Buhari

Sauyin yanayi ke haddasawa Matasan Najeriya ƙaura zuwa 'Kasashen Turai - Buhari

Za ku ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana yadda sauyin yanayi ya kasance daya daga cikin ababe dake da tasiri wajen haddasawa Matasa ƙauracewa Najeriya domin hijira da ba ta bisa ka'ida zuwa 'Kasashen Turai.

Shugaba Buhari ya bayyana sauyin yanayi cikin jerin ababen da suke haddasawa Matasan Najeriya ƙaura zuwa kasashen Turai. Sauran ababen kamar yadda shugaba Buhari ya bayyana sun hadar da; rashin tsaro, ilimi da kuma nakasun kula da harkokin kiwon lafiya da sauransu.

Cikin wata sanarwa da sanadin mai magana da yawun shugaban kasa, Mista Femi Adesina, shugaba Buhari ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da Mista Toni Iwobi, dan asalin kasar Najeriya dake rike da kujerar Sanata a majalisar dattawa ta kasar Italia.

Shugaba Buhari tare da Sanata Iwobi a tsakiya hoton bayan ganawarsu

Shugaba Buhari tare da Sanata Iwobi a tsakiya hoton bayan ganawarsu
Source: Facebook

Ganawar a ranar Alhamis din da ta gabata tsakanin shugaba Buhari ta Mista Iwobi ta gudana ne a wani bangare na daban da taron majalisar dinkin duniya karo na 73 dake ci gaba da gudana a birnin New York na kasar Amurka.

KARANTA KUMA: 'Kasashen ƙetare ke ƙarfafa rashawa a nahiyyar Afirka - Buhari

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, shugaba Buhari ya gana tare da Mista Iwobi da kuma tawagar wakilan majalisar dattawan kasar ta Italiya, inda suka tattauna yadda sauyin yanayi ke haddasa barazanar ƙaura zuwa kasashen Turai a tsakankanin Matasan Najeriya.

Tawagar dattawan kasar Italiya ta kuma tattauna al'amurran da za su kawo karshen yadda ake ribatuwa da Tafkin Chadi wajen ƙaura da ba bisa ka'ida ba, inda kuma suka gabatarwa da shugaba Buhari shirye-shiryensu na ziyartar Najeriya na ba da jimawa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel