'Kasashen ƙetare ke ƙarfafa rashawa a nahiyyar Afirka - Buhari

'Kasashen ƙetare ke ƙarfafa rashawa a nahiyyar Afirka - Buhari

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari, cikin fushi da nuna damuwarsa ya bayyana ababen da suke kara ta'azzara annobar cin hanci da rashawa a ilahirin fadin nahiyyar Afirka.

Shugaban kasar a ranar Juma'ar da ta gabata ya bayyana cewa, wau miyagun al'ummar nahiyyar Afirka na hada gwiwa da wasu ƙasashen ƙetare waje ƙulla kutungwilar ƙarfafa rashawa a nahiyyar Afirka.

Cikin wata sanarwa da sanadin mai magana da yawun shugaban kasa, Mista Femi Adesina, ya bayyana cewa Buhari ya bayyana hakan ne yayin halartar wani taro kan yadda cin hanci da rashawa ke barazanar zagon kasa ga ci gaban nahiyyar Afirka.

'Kasashen ƙetare ke ƙarfafa rashawa a nahiyyar Afirka - Buhari

'Kasashen ƙetare ke ƙarfafa rashawa a nahiyyar Afirka - Buhari
Source: UGC

Legit.ng ta fahimci cewa, an gudanar da wannan taro cikin birnin New York a wani bangare na daban da babban taron majalisar dinkin duniya karo na 73 da ake gudanarwa a kasar Amurka.

A yayin taron wanda cibiya ta dandalin ci gaban Afirka ta gudanar shugaba Buhari ya bayyana cewa, akwai bukatar tsayuwar daka da jajircewa daga bangaren shugabannin nahiyyar Afirka domin tsarkaka daga wannan mummunar annoba ta rashawa da ta yiwa yankin katutu.

KARANTA KUMA: PDP ba za ta tarwatse ba koda bayan Zaben fidda Gwani - David Mark

Wannan annoba ta da zamto tamkar karfen kafa a nahiyyar Afirke ta na ci gaba da ciwa shugaba Buhari Tuwo a 'Kwarya dangane da yadda ake yasa tare da tsotse dukiyar al'ummar kasashen Afirka zuwa kasashen ketare musamman dukiyar al'ummar Najeriya.

Sai dai shugaba Buhari ya bayyana farin cikinsa dangane da yadda shugabannin kasashen Afirka suka mike tsaye wurjanjan domin tabbatar da gaskiya da aminci yayin gudanar da harkokin shugabanci a kasashen su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel