Kuma dai: Wasu Ministocin Buhari 7 da basu da takardar NYSC

Kuma dai: Wasu Ministocin Buhari 7 da basu da takardar NYSC

A cikin 'yan kwanakin nan ne aka gano cewa biyu daga cikin Ministocin shugaba Muhammadu Buhari ba su yi hidimar kasa da dokar kasa ta wajabta a kan dukkan 'yan kasa ba, har ma akwai hukucincin zuwa gidan yari ga wanda shekarunsa ba su haura ba amma ya ki zuwa.

Bincike da Premium Times ta yi ya nuna cewa Ministan Kudi Kemi Adeosun da Ministan Sadarwa Adebayo Shittu ba suyi hidimar kasar ba kuma dokar kasa ba ta yafe musu ba saboda ba su bi ka'idojin da ake bukata ba.

A yayin da an tilastawa Adeosun yin murabus, jam'iyyar APC ta kanta da hana Adebayo Shittu takara saboda kaucewa abinda zai iya faruwa a gaba.

Kuma dai: Wasu Ministocin Buhari 7 da basu da takardar NYSC

Kuma dai: Wasu Ministocin Buhari 7 da basu da takardar NYSC
Source: UGC

Wata bincike da Premium Times tayi ya nuna cewa wasu ministocin Buhari 6 ba su da takardan kammala NYSC kafin a nada su mukamansu a 2015 sai dai su ba su karya doka ba saboda shekarunsu ne ya wuce 30 lokacin da suka kammala digiri, wasu kuma sunyi aikin soja wanda hakan ya dauke musu hidimar kasar.

Ministocin da ba su da takardun NYSC sune da kuma dalilan da yasa ba suyi hidimar kasar

1) Minsitan Ayyukan Noma Audu Ogbeh - Shekarunsa ya haura 30 lokacin da ya kammala digiri

2) Karamin MInsitan Lafiya, Osagie Ehanire - Ba'a kafa dokar NYSC lokacin da ya kammala digirinsa

DUBA WANNAN: Zaben Osun: Yarjejeniyar da muka kula da Omisore - Oshiomhole

3) Karamin Minsitan Ilimi, Anthony Anwuka - Shekarunsa sun haura na yin hidimar kasa

4) Karamin Ministan Gidaje, Mustapha Shehuri - Ya kammala digiri yana da shekaru 46

5) Ministan Muhalli, Amina Mohammed - Ba tayi karatun digiri ba

6) Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika - Ya yi karatun koyon tukin jirgi ne wanda ba dai-dai ya ke da digiri ba

7) Ministan Harkokin Cikin Gida, Abdulrahman Dambazau - Aikin soja da ya yi ya dauke masa hidimar kasa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel