Zaben fitar da gwani: Buhari ya samu kuri'u 388,653 a jihar Rivers

Zaben fitar da gwani: Buhari ya samu kuri'u 388,653 a jihar Rivers

- Buhari ya samu kuri'u 388,653 a zaben fidda gwani a Rivers wadda ya dara 202,599 da shugaban kasar ya samu a Jigawa

- An yi amfani da tsarin karo bayan kato ne wajen gudanar da zaben

- Rahotanni sun bayyana cewa jami'an hukumar INEC sun hallarci yadda aka gudanar da zaben

A ranar Juma'a, 28 ga watan Satumba ne jam'iyyar APC ta gudanar da zaben fitar da gwani na takarar kujerar shugabancin kasa a jam'iyyar inda a jihar Rivers aka gudanar da zaben a mazabu 319 kamar sakataren yada labarai na jihar, Mr Chris Finebone ya sanar a Fatakwal

Mr Finebone ya ce ministan sufuri, Chibuike Ameachi yana daga cikin wadanda suka hallarci zaben na fitar da gwani.

Zaben fitar da gwani: Buhari ya samu kuri'u 388,653 a jihar Rivers

Zaben fitar da gwani: Buhari ya samu kuri'u 388,653 a jihar Rivers
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Babban magana: 'Yan sanda sun damke dan fashi sanye da khakin sojoji

A cewar Finebone, mambobin jam'iyyar 388,653 ne a sassa daban-daban da ke jihar suka zabi shugaba Muhammadu Buhari a matsayin dan takarar shugaban kasa da suke so.

"An gudanar da zaben ne ta hanyar amfani da tsarin kato bayan kato kamar yadda kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ta amince da shi.

"Jami'an hukumar zabe mai zaman kanta INEC da ke kananan hukumomi 23 da ke jihar sun hallarci inda ake zabukan.

"Kazalika, jami'an 'yan sanda sun hallarci wuraren da ake gudanar da zabukan domin tabbatar da cewa komi ya tafi lafiya kalau," inji Fishbone.

Mr Ameachi wanda shine jam'in zabe na jihar ya fara ziyarar sakatariyar jam'iyyar kafin ya ziyarci mazubu da ke Fatakwal da kewaye domin ganewa idanunsa yadda abubuwa ke wakana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel