Ban taba tunanin wanda na sace zai gudu ba - Wani mai garkuwa da mutane

Ban taba tunanin wanda na sace zai gudu ba - Wani mai garkuwa da mutane

- Asarin wani mai garkuwa da mutane da tonu bayan daya daga cikin wanda suka sace ya tsere

- Masu garkuwa da mutanen sun bige da barci ne a yayin da wanda a kayi garkuwar da shi ya sulale ya gudu

- Daga bisani ya kai kara wajen 'yan sanda kuma jami'an 'yan sandan suka damke daya daga cikin masu garkuwa da mutanen

Hukumar 'yan sanda na jihar Niger ta ce jami'anta sunyi nasarar kama wani Abdullahi Shuaibu mai shekaru 22 da ya yi garkuwa da wani Bello Umar mazaunin kauyen Vunu da ke karamar hukumar Lavun ta jihar.

Jami'an 'yan sandan Lemu sun bi sahun Shuaibu sun kama shi ne bayan daya daga cikin wanda a kayi garkuwa dashi ya samu ya tsere daga inda suka ajiye shi a yayin da masu gadinsa ke barci.

Ban taba tunanin wanda na sace zai gudu ba - Wani mai garkuwa da mutane

Ban taba tunanin wanda na sace zai gudu ba - Wani mai garkuwa da mutane

DUBA WANNAN: Babban magana: 'Yan sanda sun damke dan fashi sanye da khakin sojoji

An gano cewa Shuaibu sun sace Umar ne daga kauyen su a cikin watan Augustan bara tare da taimakon wasu mambobin kugiyar na su ta satar mutane guda uku.

"Ban taba tsamanin cewa wanda muke garkuwa da shi zai iya tserewa ba, da mun san hakan da tuni mun karbi kudin fansar mu a maimakon yanzu da 'yan sanda suka kama ni.

"Barce ce ta kwashe mu shi kuma wanda muke garkuwa da shi ya tsere. Daga bisani ya kai kara ofishin 'yan sanda kuma aka kama mu daga baya," inji Shuaibu.

Kakakin hukumar 'yan sandan jihar, Muhammad Abubakar ya ce 'yan sandan sun baza jami'ansu domin kamo sauran mambobin kungiyar garkuwa da mutane da ke aiki tare da Shuaibu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel