Zaben Osun: Yarjejeniyar da muka kula da Omisore - Oshiomhole

Zaben Osun: Yarjejeniyar da muka kula da Omisore - Oshiomhole

- Ciyaman din APC, Adams Oshiomhole ya bayyana yarjejeniyar da suka kula da Sanata Iyiola Omisore na SDP

- Oshiomhole ya ce yarjejeniyar da suka kula ne dalilin da yasa jam'iyyar APC tayi nasara a zaben raba gardamar na Osun

- Oshiomhole ya ce APC tayi alkawarin bawa Omisore kujerar takarar Sanata da na Majalisar wakilai

A yayin da jam'iyyar APC ke murnar nasarar da ta samu na lashe zaben raba gardama na kujerar gwamna a jihar Osun, Ciyaman din jam'iyyar na kasa, Comrade Adams Oshiomhole ya ce jam'iyyar tayi nasara ne saboda yarjejeniyar da ta kula da dan takarar gwamna na SDP, Sanata Iyola Omisore.

Zaben Osun: Yarjejeniyar da muka kula da Omisore - Oshiomhole

Zaben Osun: Yarjejeniyar da muka kula da Omisore - Oshiomhole
Source: Facebook

Oshiomhole ya ce yayin da jam'iyyar PDP ta mayar da hankalinta wajen ganin cewa ta dakatar da gudanar da zabeb raba gardamar, APC ta mayar da hankali wajen tattaunawa da dan takarar SDP, Sanata Iyiola Omisore.

DUBA WANNAN: Mai rabo ka dauka: APC ta amince da takarar mutane 3 da ke burin kayar da gwamna Abubakar

"Gaskiya ne mun amince za mu bashi damar takarar kujerar Sanata, za kuma mu bashi damar takarar kujerar majalisar wakilai. Bayan haka zamu tattauna yadda za muyi aiki tare," inji Oshiomhole.

Ya kara da cewa Omisore mataimakin gwamnan ne ga daya daga cikin wadanda suka kafa APC, Cif Bisi Akande a shekarar 1999, ya ce tun a baya Omisore ya kasance yana aiki tare da mutane masu son ganin cigaban al'umma.

Oshiomhole ya ce babu kanshin gaskiya cikin zargin da ake na cewa jam'iyyar ta yiwa sauran kananan jam'iyyu barazana. Ciyaman din na APC ya kuma yabawa hukumar zabe mai zamanta INEC saboda aikin da ta gudanar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel